Akalla mayaka 49 na kungiyar ta’addanci ta Jam’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihād da suka hada da Kwamandoji biyu, Ba’a Usman (Munzir) da Alhaji Ari (Nakib), sun mika wuya ga sojoji.
A cewar Zagazola Makama, wani mai sharhi kan harkokin tsaro kuma kwararre kan yaki da ta’addanci a tafkin Chadi, majiyoyin tsaron soji sun ce ‘yan ta’addar sun mika wuya ga sojojin Operation Hadin Kai da ke Damboa a ranar 20 ga watan Nuwamba, 2022.
- Har Yanzu Jama’a Ba Su Saki Jiki Da Tubabbun Boko Haram A Jihar Borno Ba
- An Mayar Da Tubabbun Mayakan Boko Haram 3,500 Unguwanninsu A Jihar Borno
Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa maharan sun fito ne daga dajin Sambisa, inda suke fakewa tare da kaddamar da aiyukansu na ta’addanci a jihar.
LEADERSHIP ta rawaito cewa kawo yanzu akalla ‘Yan tada kayar baya 90,000 da suka hada da mayaka da ‘Yan bindiga da iyalansu suka mika wuya ga Sojojin Nijeriya.
Majiyar ta yi nuni da cewa, ci gaba da kai hare-hare kan maharan a karkashin kulawar sojojin Nijeriya, ke sa su mika wuya.