Kwamishinan yada labarai, al’adu da yawon bude ido na jihar Benue, Mathew Abo, wanda aka yi garkuwa da shi a gidansa da ke Zaki-Biam a ranar Lahadi, 24 ga Satumba, 2023, ya kubuta.
Majiya mai tushe, ta bayyana cewa wadanda suka sace Abo sun sako shi da sanyin safiyar ranar Alhamis, kuma tuni aka sada shi da iyalansa.
- Tattalin Arzikin Afirka Zai Durkushe – Bankin Duniya
- Gajiya Ce Ta Sa Na Fadi Yayin Tantance Ni A Majalisa — Balarabe
Sai dai majiyar ba ta bayyana ko an biya kudin fansa naira miliyan 60 da masu garkuwa da mutane suka nema ba.
Kwamishinan ya kwashe kwanaki 10 a tsare kafin a sake shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp