Kwamishinan tsaron cikin gida da ayyuka na musamman na jihar Kano, Manjo Janar Muhammad Inuwa Idris (mai ritaya), ya yi murabus daga mukaminsa.
An tabbatar da murabus din nasa ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar. Ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da murabus din a hukumance, inda ya nuna jin dadinsa da irin gudunmawar da Janar din sojan ya bayar a lokacin da yake gudanar da aikinsa.
- Rasha Da Ukraine Sun Amince Da Tsagaita Wuta A Tekun Black Sea
- Kasuwar Kayayyakin Masarufi Ta Sin Za Ta Ci Gaba Da Nuna Yanayin Bunkasa Bisa Daidaito A Bana
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, Manjo janar Idris (mai ritaya) shi ne mamba na biyu a majalisar zartarwa ta jihar Kano da ya mika takardar murabus dinsa a shekarar 2025. In ba a manta ba, kwamishinan sa ido da tantance ayyuka, Mohammed Diggol, shi ma ya yi murabus a farkon wannan shekarar.
An nada Manjo Janar Idris ne a watan Agustan 2024 a matsayin kwamishinan sabuwar ma’aikatar da aka kirkiro. A cikin dan kankanin wa’adinsa, ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa tsarin gudanar da ayyukan ma’aikatar.
A cikin sanarwar a hukumance, gwamna Yusuf ya yabawa Manjo janar Idris bisa jajircewarsa da yi wa jihar hidima. “Muna godiya ga Manjo Janar Muhammad Inuwa Idris (mai ritaya) bisa jajircewa da bayar da gudunmawa wajen ci gaban jihar Kano tun daga lokacin da ya ke aikin soja, muna masa kyakkyawan fata a cikin sabuwar rayuwarsa ta gaba,” in ji gwamnan.
Duk da cewa ba a bayar da wani dalili na murabus din nasa na ba zato ba tsammani ba, gwamnan ya bayyana kwarin gwiwar cewa, magajinsa zai dora kan harsashin da Idris ya kafa domin ganin ma’aikatar ta yi aiki yadda ya kamata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp