Fadar Gidan Gwamnatin Amurka (WhiteHouse), ta ce Rasha da Ukraine sun amincewa Jiragen jigilar kayayyakin kasuwanci gudanar da zirga-zirga cikin aminci a tekun Black Sea ba tare da kai musu hare-haren soji ba.
Amurka ta fitar da wannan sanarwar ne bayan jami’an Amurka sun gana da wakilan kasashen biyu a Saudiyya a ranar Talata.
- Dole Ne A Tauna Tsakuwa Don Aya Ta Ji Tsoro
- Sin Na Ci Gaba Da Kasancewa Cibiyar Rarraba Hajojin Da Masana’antu Ke Sarrafawa
Sai dai Rasha ta ce, dole ne a dage wasu takunkuman da aka sanya wa bankuna, kamfanonin inshora, da masu fitar da abinci, kafin yarjejeniyar tsagaita bude wutar ta fara aiki.
Sai dai, Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya zargi Rasha da “kwarara karya” game da sharuddan yarjejeniyar.
Rahotanni sun ce shugaban Amurka Donald Trump na ganawa da jakadun Amurka a fadar White House kan lamarin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp