Kwamishinan ‘yansandan jihar Zamfara, Muhammad Shehu Dalijan, a madadin Sufeto Janar na ‘yansandan, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, ya gabatar da cek din Naira miliyan 50,145,119.83 ga iyalai 27 na jami’an da suka rasu a lokacin da suke bakin aiki.
Wadannan cek da aka bayar wani bangare ne na shirin IGP a karkashin tsarin inshora don taimaka wa iyalan jami’an da suka rasu.
- DSS Ta Ceto Mutane 7 Da Aka Sace A Sakkwato
- Marafa Ga Matawalle: Girmama Tinubu Ba Matsalar Nijeriya Ba Ce
Kakakin rundunar, ASP Yazid Abubakar, ya ce Kwamishinan ya bayyana haka a takardar ya sanya wa hannu ga manema labarai a Gusau.
A cewar Yazid, ya yaba wa IGP bisa wannan karamci da ya nuna, sannan ya kuma yi kira ga iyalan jami’an da suka rasu da su yi amfani da kudin da kyau da kuma kula da iyalansu.
Malam Yahaya Umar daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin a jawabinsa a madadin sauran wadanda suka amfana, ya gode wa babban Sufeton ‘yansanda da rundunar ‘yansandan jihar bisa wannan tallafi.
Ya kuma bayar da tabbacin cewa za su kashe kudaden da aka ba su ta hanyar da ta dace.