Kasancewa a kullum al’amuran da suka shafi harkar Mai a kasar na kara canza fasali da durkushewa, Majalisar Wakilai ta Tarayyar Nijeriya ta dauki matakin nemo hanyar warware matsalar da ake fuskanta ta hanyar kafa kwamiti mai bincike a kan tallafin man.
Shugaban kwamitin, Dan Majalisar Tarayya Mai wakiltar Mazabar Wurno da Raba, Honarabul Ibrahim Almustapha Aliyu da ya Jagoranci zaman kwamitin, ya bayyana cewa akwai shirye-shirye da tsare-tsaren da suka gudanar domin tabbatar da an samu mafita a cikin lamarin.
Kwamitin binciken ya gayyaci babban hafsan mayakan sojojin ruwa wato Nigerian Navy Wanda Rear Admiral Emmanuel Ogala ya wakiltar domin suna cikin masu ruwa da tsaki na harkan Mai a Kasar nan.
Da yake zantawa da Manema Labarai bayan zaman kwamitin, Honarabul Ibrahim ya ce tun daga lokacin da aka kafa kwamitin a ranar 23 ga watan Yuli, kwamitin ya fara tsare-tsare da gudanar da bincike a kan wadanda ke da ruwa da tsaki a kan harkar domin zakulo abin da yake matsalar.
Ya ce “ba wai mun fito ido rufe ba ne na neman masu laifi, amma duk wani dan kasa harkar mai tana damun shi domin ya kamata a sassauta wa ‘yan Æ™asa amma bai kamata a saka ido a bar abubuwa na tabarbarewa ba.”
“Kasa na neman kuÉ—i domin a inganta harkar noma, harkar Ilimi, harkar sufuri, samar da ruwan sha da shinfida tituna, amma an Kasa gane inda aka dosa.”
“Wato duk abin da ake yi na gudanar da wata hada-hada kuma ya kamata a yi shi a bisa Doka. Hukumar yin rajistar kamfanoni da hukumar NNPC su suka san duk wadanda suka cancanta.”
“Sai wadanda suka yi hulda da su sun zo sun ba mu bayanai, shi ya sa sai NNPC da ta shiga hulda da su sun zo sun yi mana bayani domin ta yu abinda muke tunani ba shi ne ba.”
A cewarsa, mai yiwuwa tallafin ya amfani ‘yan Nijeriya ba tare da al-mubazaranci ba, ko hasara kamar yadda mutane suke hasashen hakan.
A karshe kwamitin ya bukaci rundunar mayakan ruwa na ƙasar nan da ta kawo wasu muhimman bayanai a gaban kwamitin domin su ci gaba da ayyukan su.
Tun da farko ɗaya daga cikin kamfanoni Masu aikin Mai a ƙasar nan wato Hab Energy Limited karkashin jagorancin Abdulwahab Oseni sun bayyana a gaban kwamitin inda su ma aka bukaci Karin bayanai daga gare su
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp