Da safiyar yau Talata 31 ga Disamban 2024, kwamitin kasa na Majalisar Ba Da Shawarwari Kan Harkokin Siyasa na Kasar Sin, watau CPPCC, ya gudanar da kwarya-kwaryan bikin maraba da sabuwar shekara ta 2025 a babban zauren taronsa, inda Shugaba Xi Jinping ya halarci bikin tare da gabatar da muhimmin jawabi.
A cikin jawabinsa, Shugaba Xi ya bayyana cewa, a shekarar da ta gabata, Majalisar Ba Da Shawarwarin Siyasa ta Kasar Sin ta aiwatar da matakai da tsare-tsaren kwamitin koli na CPC sau da kafa, tare da sauke nauyin ayyukan da aka dora masa a matakin kasa, da karfafa gina kansa da kuma bayar da sababbin gudummawa masu yawa ga bunkasa ci gaban kasa.
Shugaba Xi ya ce, a sabuwar shekara ta 2025, kasar Sin za ta zurfafa gyare-gyarenta a dukkan fannoni, da fadada matakin bude kofa a babban matsayi ga kasashen duniya, da inganta tsare-tsaren kawo ci gaba da tsaurara tsaro, da aiwatar da karin manufofi masu karsashi da manyan harkokin tattalin arziki.
Kazalika, shugaban ya ba da tabbacin dorewar farfado da tattalin arziki da kara azamar ci gaba da inganta jin dadin rayuwar al’umma a sabuwar shekarar. (Abdulrazaq Yahuza Jere)