• English
  • Business News
Saturday, June 28, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kwamitin Kolin JKS Ya Amince Da Kudurin Kara Zurfafa Sauye-sauye Daga Dukkanin Fannoni

by Sulaiman and CGTN Hausa
12 months ago
in Daga Birnin Sin
0
Kwamitin Kolin JKS Ya Amince Da Kudurin Kara Zurfafa Sauye-sauye Daga Dukkanin Fannoni
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Kwamitin kolin JKS na 20 ya amince da kudurin kara zurfafa sauye-sauye daga dukkanin fannoni, da nufin bunkasa zamanantarwa irin ta Sin. An amince da kudurin ne a cikakken zaman kwamitin na 3 da ya gudana tsakanin ranaikun Litinin zuwa Alhamis din nan.

Ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ne ya jagoranci zaman. Kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya gabatar da muhimmin jawabi, kamar dai yadda wata sanarwar bayan taron da aka fitar a yau Alhamis ta bayyana.

  • Shugaban Amurka, Joe Biden Ya Kamu Da Cutar Covid-19
  • Sin Za Ta Tallafawa Kamfanonin Gida Da Na Waje A Fannin Sabunta Na’urori Da Yin Musayar Tsoffin Kaya Da Sabbi

Yayin zaman, an saurari, tare da tattauna batutuwan da suke kunshe cikin wani rahoto kan ayyukan ofishin siyasa na kwamitin kolin karkashin jagorancin shugaba Xi, a madadin ofishin siyasar, tare da nazari, da amincewa da kudurin kwamitin kolin na JKS don gane da kara zurfafa sauye-sauye daga dukkanin fannoni, da nufin bunkasa zamanantarwa irin ta Sin. Shugaba Xi ya yi fashin baki don gane da sassan kudurin da aka amince da shi.

A cewar sanarwar bayan taron, makasudin zurfafa sauye-sauye daga dukkanin fannoni ya hada da ci gaba da kyautatawa, da bunkasa tsarin gurguzu mai halayyar musamman na kasar Sin, da zamanantar da tsarin tafiyar da harkokin kasa, da karfafa kwarewar jagoranci.

Kaza lika, sanarwar ta kara da cewa, ya zuwa shekarar 2035, za a kai ga gina managarcin tsarin raya tattalin arziki irin na gurguzu daga dukkanin fannoni, da kara inganta tsarin na gurguzu mai salon musamman na Sin, da zamanantar da daukacin tsarinmu, da ikon aiwatar da jagoranci, da cimma salon zamanantarwa na gurguzu”.

Labarai Masu Nasaba

An Horas Da Kwararrun Ma’aikata Sama Da Dubu 500 Karkashin Hadin Gwiwar Sin Da Sassan Kasa Da Kasa A Fannin Inganta Kwarewar Ma’aikata

Sin Na Kokarin Gaggauta Taimakawa Kasashen Afirka Da Kara Hadin Gwiwa Da Su

Dukkanin wadannan za su kafa ginshiki mai karfi na gina kasar Sin, yadda za ta zama mai bin salon gurguzu na zamani a dukkanin fannoni nan zuwa tsakiyar karnin nan da muke ciki.

Za a kammala daukacin ayyukan sauye-sauyen da aka fayyace cikin kudurin ne nan zuwa lokacin bikin cikar jamhuriyar jama’ar kasar Sin shekaru 80 da kafuwa a shekarar 2029. (Saminu Alhassan)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: JKSshugaban kasar Sin Xi JinpingSin
ShareTweetSendShare
Previous Post

Babu Ɗalibin Da Zai Sake Shiga Jami’a Sai Ya Cika Shekaru 18 

Next Post

Sabon Tsarin Karatun Sakandare Zai Fito A Watan Satumba – Minista

Related

An Horas Da Kwararrun Ma’aikata Sama Da Dubu 500 Karkashin Hadin Gwiwar Sin Da Sassan Kasa Da Kasa A Fannin Inganta Kwarewar Ma’aikata
Daga Birnin Sin

An Horas Da Kwararrun Ma’aikata Sama Da Dubu 500 Karkashin Hadin Gwiwar Sin Da Sassan Kasa Da Kasa A Fannin Inganta Kwarewar Ma’aikata

10 minutes ago
Sin Na Kokarin Gaggauta Taimakawa Kasashen Afirka Da Kara Hadin Gwiwa Da Su
Daga Birnin Sin

Sin Na Kokarin Gaggauta Taimakawa Kasashen Afirka Da Kara Hadin Gwiwa Da Su

18 hours ago
Sin Da Amurka Sun Tabbatar Da Bayanan Tsarin Aiwatar Da Matsayar Da Aka Cimma Yayin Tattaunawar Cinikayya A Geneva
Daga Birnin Sin

Sin Da Amurka Sun Tabbatar Da Bayanan Tsarin Aiwatar Da Matsayar Da Aka Cimma Yayin Tattaunawar Cinikayya A Geneva

19 hours ago
Xinjiang Ta Bude Hanyar Jigilar Kayayyaki Ta Kasa Da Kasa Zuwa Afirka Ta Farko
Daga Birnin Sin

Xinjiang Ta Bude Hanyar Jigilar Kayayyaki Ta Kasa Da Kasa Zuwa Afirka Ta Farko

20 hours ago
Lai Cing-te Ba Zai Cimma Nasarar Kalubalantar Dokar Kasa Da Kasa Ba
Daga Birnin Sin

Lai Cing-te Ba Zai Cimma Nasarar Kalubalantar Dokar Kasa Da Kasa Ba

21 hours ago
Abin Da Ya Sa Muke Ci Gaba Da Tuntubar Kasar Sin A Kai A Kai
Daga Birnin Sin

Abin Da Ya Sa Muke Ci Gaba Da Tuntubar Kasar Sin A Kai A Kai

22 hours ago
Next Post
Sabon Tsarin Karatun Sakandare Zai Fito A Watan Satumba – Minista

Sabon Tsarin Karatun Sakandare Zai Fito A Watan Satumba - Minista

LABARAI MASU NASABA

An Horas Da Kwararrun Ma’aikata Sama Da Dubu 500 Karkashin Hadin Gwiwar Sin Da Sassan Kasa Da Kasa A Fannin Inganta Kwarewar Ma’aikata

An Horas Da Kwararrun Ma’aikata Sama Da Dubu 500 Karkashin Hadin Gwiwar Sin Da Sassan Kasa Da Kasa A Fannin Inganta Kwarewar Ma’aikata

June 28, 2025
Tarihin Yadda Cinikin Bayi Ya Fara A Nahiyar Afirka (3)

Tarihin Yadda Cinikin Bayi Ya Fara A Nahiyar Afirka (3)

June 28, 2025
An Kai Wa Magoya Bayan Atiku Hari A Gombe

Rasuwar Dantata Babban Rashi Ne Ga Afirka – Atiku

June 28, 2025
Sin Ta Samu Nasarorin A Zo A Gani Wajen Yaki Da Miyagun Kwayoyi

Sin Ta Samu Nasarorin A Zo A Gani Wajen Yaki Da Miyagun Kwayoyi

June 28, 2025
Kula Da  Kanki Bayan Haihuwa Abu Ne Muhimmi 4

Kula Da  Kanki Bayan Haihuwa Abu Ne Muhimmi 4

June 28, 2025
Mata Ku Kula Da Masu Tallan Maganin Hana Kishiya

Mata Ku Kula Da Masu Tallan Maganin Hana Kishiya

June 28, 2025
Rasuwar Ɗantata Babban Rashi Ne Ga Nijeriya –  Shugaban ƘasaTinubu

Rasuwar Ɗantata Babban Rashi Ne Ga Nijeriya –  Shugaban ƘasaTinubu

June 28, 2025
Hanyar Da Matasa Za Su Bi Don Ceto Demokuradiyyar Nijeriya Daga Rugujewa

Ƙoƙarin Ƙungiyoyin Afrika A Gasar Kofin Duniya

June 28, 2025
Bam Ya Kashe Mutane 4, Ya Jikkata 21 A Yobe

Bam Ya Kashe Mutane 4, Ya Jikkata 21 A Yobe

June 28, 2025
Hanyar Da Matasa Za Su Bi Don Ceto Demokuradiyyar Nijeriya Daga Rugujewa

Hanyar Da Matasa Za Su Bi Don Ceto Demokuradiyyar Nijeriya Daga Rugujewa

June 28, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.