Kwamatin Majalisar Dattawa da ke nazari kan dokar zabe, ya bayar da shawarar rage wa ‘yan majalisa albashi da kuma masu mukaman gwamnati.
Shugaban kwamatin, Sanata Sharafadeen Ali ne, ya bayyana hakan a ranar Litinin.
Ya bayyana hakan ne, yayin da gana da ‘yan siyasa da kuma wakilai a bangaren shari’a game da aikin kwamitinsa na yi wa dokar zabe ta 2022 kwaskwarima.
Ya ce suna bayar da shawarar rage albashin ‘yan majalisar da kashi 30 cikin 100, yayin da za a rage na masu rike da mukamai da kashi 40 domin rage kashe kudin gudanar da gwamnati.
Yayin ganawar, jam’iyyun siyasa sun nemi a dinga gudanar da zabukan shugaban kasa, da na ‘yan majalisar tarayya, da gwamnoni, da ‘yan majalisar jiha a rana daya.
A cewarsu, hakan zai rage kashe kudi a lokacin zabe.
Jam’iyyun sun kuma nemi a hada katin zabe da lambar dan kasa ta NIN domin kara tsaro da kuma rage kashe kudi wajen yin rajistar katin zabe.
A baya-bayan nan dai gwamnatin tarayya ta kara wa’adin hada layukan waya da lambar NIN zuwa karshen watan Satumba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp