Kwamitin wucin gadi da majalisar dokokin Jihar Kaduna ta kafa domin binciken duk wasu kudade da bashin da aka ciyo wa jihar, karkashin tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai ya mika rahotonsa ga majalisar.
Da yake gabatar da rahoton yayin zaman majalisar na ranar Laraba, shugaban kwamitin wucin gadi, Henry Zacharia, ya ce yawancin bashin da aka ciyo a karkashin gwamnatin El-Rufai ba a yi amfani da su domin abin da aka karbo bashin domin su ba.
- Napoli Ta Nada Antonio Conte A Matsayin Sabon Kocinta
- Saurayi Da Budurwarsa Sun Sace Kayan Lefen ’Yar Uwarsa A Kano
Da yake karbar rahoton, kakakin majalisar dokokin Kaduna, Yusuf Liman, ya bayyana cewa gwamnatin El-Rufai ta karkatar da Naira biliyan 423, wanda hakan ya bar jihar cikin kangin bashi.
Don haka kwamitin ya bayar da shawarar a binciki El-Rufai tare da gurfanar da wasu daga cikin gwamnatinsa don tuhumar su bisa karkatar da kudade da kuma bayar da kwangiloli ba bisa ka’ida ba.
Kwamitin ya kuma bayar da shawarar dakatar da kwamishinan kudi na jihar Kaduna, Shizer Badda, wanda yayi aiki da gwamnatin El-Rufai a baya, da kuma shugaban hukumar ilimi a matakin farko na jihar.
Har ila yau, ya bayar da shawarar yin cikakken bincike kan wasu da suka rike manyan mukamai a gwamnatin bayan ga hukumomin yaki da cin hanci da rashawa.
Kwamitin da majalisar dokokin Jihar Kaduna ta kafa, an dora wa nauyin yin bincike kan bashi da tallafi da ayyukan da aka aiwatar daga shekarar 2015 zuwa 2023 karkashin gwamnatin El-Rufai.