Kwamitin tantance ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya kori mutane 10 daga cikin 23 da suka nemi takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023.
Shugaban kwamitin kuma tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Cif John Odigie-Oyegun, ne ya bayyana hakan a sakatariyar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja, kwamitin ya gabatar da rahotonsa a yammacin ranar Juma’a.
Don haka, 13 cikin masu neman takarar shugaban kasa ne kadai za su shiga zaben na babban taron jam’iyyar APC na kasa mai zuwa.
Sai dai Odigie-Oyegun, bai ambaci sunansu ba, yana mai cewa shugabannin jam’iyyar za su yi abin da ya kamata.
Ya kuma jaddada cewa kwamitin ya yi la’akari da samari masu neman tsayawa takara wajen gudanar da ayyukansa.
Cikakkun bayanai za su zo daga baya…