Duk da cewa ba a taba bayyana ofishin uwargidan shugaban kasa a hukumance ba kamar yadda tsarin mulki ya tanada, amma wadanda ke shiga ofishin na taka rawa sosai a harkokin siyasa da zamantakewar al’umma a matsayin matar shugaban kasa.
A Nijeriya, ofishin da aka kafa tun lokacin da aka samu ‘yancin kai ya bambamta daaga tsakanin 1985 zuwa 1993, a lokacin mulkin soja na Janar Ibrahim Babangida (mai ritaya).
- Me Ya Sa Amurka Take Maimaita Yunkurinta Na Marawa Taiwan Baya Wajen Halartar Babban Taron Kiwon Lafiya Na Duniya A Kowace Shekara?
- Kwana 6 Ga Rantsar Da Tinubu: ‘Yan Jarida Sun Yi Tsokaci Kan Yadda Aka Miƙa Mulki A Gwamnatocin Baya
Uwargidan tsohon shugaban kasa na mulkin soja, marigayiya Maryam Babangida ce ta fara nuna ado da kayan kawaa ofishin. Tun daga wannan lokacin kowace uwargidan shugaban Nijeriya tana sa ido sosai don shiga al’amuran mijinta da kuma sanin abubuwan da zai yi a nan gaba.
Duk da cewa ba a zabe ta ba ko kuma biyanta albashi, amma shaharar uwargidan shugaban Nijeriyar ya samar mata da damar da za ta rinka tasiri a harkokin siyasa.
Wasu matan shugaban kasa kan taimaki fadar shugaban kasa ta bayan fage, wasu kuma na amfani da damarsu wajen kawo sauyi ga al’amuran da suka shafi jama’a.
Sai dai yawan damar da ofishin ya samar, ya sanya wasu daga cikin matan shugabannin Nijeriya da suka shude suka shagaltu da neman mulki, lamarin da ya haifar da sukar cewa wasu daga cikinsu na da girman kai da neman mulki.
Kimanin kwanaki biyar kacal ya rage a rantsar da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu mai jiran gado, LEADERSHIP ta yi duba game da irin gudunmawar da matan shugabannin Nijeriya ke bayarwa ga gwamnatocin mazajensu tun bayan dawowar mulkin dimokradiyya a 1999.
Aisha Buhari
A shekarar 2015 lokacin da mijinta ya lashe wa’adi na farko a matsayin shugaban kasa, mutane da yawa sun yi fatan cewa Aisha Buhari mai shekara 44 a lokacin za ta kawo kwanciyar hankali da lumana a fadar shugaban kasa. Bayan shekaru takwas a kan kujerar shugaban kasa, tabbas wannan tunanin ba haka yake ba, musamman idan aka waiwayi yadda abubuwa suka faru a baya.
Aisha mai kaskantar da kai da kunya daga baya ta zama mai cacar baki da nuna karfin nuna iko. A tsawon shekaru takwas da mijinta ya yi, ta yi mu’amala da mutane da dama da ba ta kyautawa ba.
A zahiri ta ki yarda da matsayin da mijinta ya bar ta a kai wato “kula da dakin girki”.
Aisha Buhari ba wai kawai an san ta da salon kwalliyarta ba ne har ma da kyawawan ra’ayoyinta na siyasa da kalubalen rashin tsoro ga manufofin gwamnati.
Ta yi tasiri a fagen siyasa, kuma jajircewarta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ya sanya ta yi fice a Nijeriya.
Babu wanda zai yi magana a kan Aisha Buhari ba tare da ya ambaci salonta da kyawun adonta ba. A lokuta da dama adonta kan nuna isa da izza, da kuma nuna salon shigar gargajiya musamman ta Arewa.
Tufafin Aisha wani abu ne da ke nuna al’adunta, wanda galibi yana nuna launuka masu kayatarwa, sannan na gargajiya.
Duk da haka, tasirin Aisha Buhari ya wuce yanayin salonta. Ta yi amfani da kafafen sada zumunta sosai don ba da shawarar sauyin zamantakewa, ko da kuwa yana nufin kalubalantar manufofin gwamnati. Jajircewarta na fadin albarkacin bakinta a kan batutuwa masu muhimmanci ya sa ‘yan Nijeriya da dama ke girmama ta da kuma jinjina mata.
Wani abin lura da Aisha Buhari ta yi, shi ne kalubalantar manufofin gwamnati, sukar da ta yi a bainar jama’a kan tsarin zaben fidda gwani na jam’iyya mai mulki a shekarar 2018. A wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter, ta nuna rashin gamsuwarta, inda ta bayyana cewa tsarin bai dace da tsarin dimokuradiyya ba kuma babu gaskiya a ciki. Maganar da ta yi ta haifar da muhawara mai zafi a fagen siyasa, wanda ya jawo hankali ga bukatar gudanar da zabe na gaskiya da rikon amana.
Aisha ta yi tsokaci kan batutuwan da suka hada da daidaito tsakanin jinsi, ‘yancin mata da ilimi, inda ta jaddada muhimmancinsu wajen ci gaban kasa.
Ta sha nanata muhimmancin ilimi ga mata, tare da ganin cewa shi ne wani muhimmin hakki da zai iya daukaka al’umma baki daya. Ta hanyar shirinta na ‘Future Assured Initiative’, ta kaddamar da ayyuka da nufin inganta damar samun ilimi, kiwon lafiya, da damar tattalin arziki ga mata da yara a Nijeriya.
Bugu da kari kuma, fafutukar da Aisha Buhari ta yi na kare hakkin mata ya shafi yaki da cin zarafin mata. Ta yi Allah wadai da ayyukan cin zarafin mata, tare da karfafa gwiwar gwamnati da masu ruwa da tsaki da su dauki kwakkwaran matakai.
Ta hanyar muryarta ga irin wadannan batutuwa masu mahimmanci, ta taimaka wajen wayar da kan jama’a tare da yin gyare-gyaren manufofin da ke kare hakkin mata da jin dadin mata a fadin kasar nan.
Yana da kyau a lura cewa kalubalantar da Aisha Buhari ta ke yi wa manufofin gwamnati ba wai yana nufin adawa ba ne, illa dai son ganin an samu sauyi mai kyau da ci gaba a gwamnatin Buhari mai barin gado.
Ayyukanta sun nuna yadda ta himmatu wajen kyautata rayuwar ‘yan Nijeriya da kuma yunkurinta na ba da gudummawar ci gaban kasa.
Yayin da wasu na iya ganinta a matsayin wadda ba ta yarda da tsarin siyasa ba, wasu kuma suna kallonta a matsayin mai magana da hankali kuma mai ba da shawara ga wadanda suka yi fice.
Ayyukanta sun zama abin karfafawa ga daidaikun mutane, musamman mata, don amfani da muryoyinsu a kafafen yada labarai don ci gaban al’umma.
Yayin da za ta bar ofis a ranar 29 ga wata Mayu, 2023 tare da mijinta, wanda wa’adinsa na shekaru takwas zai kare a wannan rana, ta kasance fitacciyar jaruma a tarihin matan shugabannin Nijeriya.
Oluremi Tinubu
A halin yanzu, kyakkyawar matar zababben shugaban kasa mai jiran gado, Sanata Remi Tinubu, an santa da salon kwalliya don nuna irin kyawun da ta ke da shi. Mace ce ‘yar siyasa mai kishi, wacce kyawawan halayenta a matsayinta na hazika mai kula da jama’a da taimakon jama’a suna kawo rudani a zukatan takwarorinta maza.
Sanata Tinubu ta wakilci gundumar Legas ta Tsakiya a majalisar dattawa daga 1999 zuwa 2007 lokacin da mijinta ke gwamnan Legas.
Mutanen Legas sun bayyana salon Remi a matsayin mai nuna aji da bayyana kyawunta, yayin da kuma ta ke da saukin kai wajen yin mu’amala.
Wata ‘yar jarida a gidan talabijin na Legas, Kemi Muyi-Adeniyi, ta shaida wa LEADERSHIP cewa, Misis Remi Tinubu mace ce mai saukin kai kuma kyakkyawa.
Ta ce, “Na samu damar tattaunawa da ita a shirina. Mace ce mai saukin kai wacce ta ke da hazaka. Don ko shigar da ta yi a shirin mutum zai fahimci saukin kan ta.
“Misis Remi ba ta sanya kaya masu tsada ko sanya kayan ado masu tsada. Idan ka ganta da kyar za ka ganta sanye da kayan waje. Tana sa rigunanmu na nan gida. Shi ya sa nake girmama ta sosai.”
Har ila yau, wata fitacciyar ‘yar jarida, Busola Kukoyi, ta ce wani abu da mutane ba su sani ba game da Misis Remi Tinubu shi ne tana da tausayi sosai.
A cewar Kukoyi, Remi ta tsani ganin yadda mutane ke shan wahala ko shiga kunci, inda ta kara da cewa uwargidan shugaban Nijeriya mai jiran gado ba ta damu da mutum wane ne wajen taimaka masa.
Ta shaida wa LEADERSHIP cewa: “Na tuna wani lamari na musamman da ya taba faruwa. Ina wajenta ranar wata Asabar da safe. Akwai wasu samari maza da za su je Landan gasar kwallon kafa. Sun kasance tsakanin shekaru takwas zuwa 12. Kocin nasu bai samu kudin siyan tikitin jirgi ba sai suka zo wajen Misis Remi Tinubu domin ta taimaka musu. Yadda ta taimaka musu abun ya kayatar da ni.
“Duk da cewa ba ta da isassun kudi a gida don siyan tikiti gaba dayansu, ta yanke shawarar kiran wakilinta don samun tikitin ba tare da kowa ya rasa jirginsa ba.
Ko da aka tambaye ta tasirin da Remi za ta iya yi, Kukoyi ta ce, “Na san za ta zama babbar abun koyi a cikin jerin matan shugaban kasar Nijeriya.”
Stella Obasanjo
Zaman Stella Obasanjo a matsayin uwargidan shugaban kasa ba wani abu ne ra za a ce ya bayyana sosai da sosai ba duba da yanayin yadda mijinta ya kankane komai. Amma duk da haka an santa kuma ta bayyana mace mai kunya da ke yawo da kai a aske.
Wani abin da ya banbanta Stella da sauran matan shugaban kasa a tarihin Nijeriya tun dawowar dimokradiyya shi ne rashin cece-kuce a kan halinta. An yi mata aiki a ciki wanda ya yi sanadiyar mutuwarta, amma mutane da yawa na girmama ta.
Turai Yar’Adua
Lokacin da Turai Yar’adua ta kasance uwargidan shugaban kasa ta yi abubuwa da dama da ta bambamta da sauran. Duk da yanayin rashin lafiyar mijinta, ta ci gaba da gudanar da ayyukanta kamar yadda ta saba. Wasu sun zarge ta da jagorantar wani katafaren gida da ke kare wasu mutane daga tuhuma.
Patience Jonathan
Patience Jonathan za a iya cewa ita ce uwargidan shugaban kasa wadda aka tafka cece-ku-ce a kanta saboda rashin sanin makamar aiki da ta ke da shi.
Uwargidan tsohon shugaban kasar ta kasance mace ce da ke sanya ‘yan Nijeriya nishadi ta hanyar tafka kura-kurai a turancinta.
Masoyanta kan kira ta da ‘Mama Peace, ta yi tasiri sosai a tsohuwar gwamnatin tarayya karkashin jam’iyyar PDP.
Daya daga cikin muhimman abubuwan da ta yi a matsayin matar shugaban kasa, shi ne ranar 12 ga watan Yuli, 2012, lokacin da tsohon Gwamna Seriake Dickson ya nada ta a matsayin babbar sakatariya a Jihar Bayelsa.
Duk da cewa aikin uwargidan shugaban kasa ba shi da tasiri a kundin tsarin mulki, amma Nijeriya ta yi matan shugaban kasa da suka nuna izza a ofishin.