Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya sallami kwamishinan ayyuka da sufuri na jihar, Hon. Tasi’u Danɗangoro da Sakatarori guda biyu da kuma shugaban hukumar jin dadin alhazai ta jihar ta Katsina.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Katsina, Alhaji Muntari Lawal ya sanya wa hannu kuma aka raba wa manema labarai ciki harda LEADERSHIP Hausa.
Sanarwar ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne domin kawo wasu sauye- sauye a gwamnatin jihar Katsina.
Manyan Sakatarorin da aka sallama sun haɗa da Alhaji Aminu Waziri, baban sakatare a ma’aikatar gona da albarkatun ƙasa da Hajiya Fatima Ahmad, babar sakatariya a ma’aikatar kula da maradun ƙarni ta jihar Katsina.
Sai kuma shugaban hukumar jin dadin da walwala ta alhazan jihar Katsina Hon. Yusuf Barmo.
Haka kuma sanarwar ta umarci duk waɗanda aka sallama da su mika ragamar tafiyar da ma’aikatunsu ga manyan daraktocin ma’aikatun ba tare da ɓata lokaci ba.
Wasu daga cikin mutanen Katsina dai na mamakin yadda wannan sallama ta zo kwana biyu da kammala zabe, inda ake ganin watakila abin ba zai rasa nasaba da yadda ta kaya a zaɓen shugaban ƙasan da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata ba.