Jam’iyyar PDP a jihar Sakkwato ta bukaci Hukumomin Yaki da Cin Hanci da Rashawa na EFCC da ICPC da su binciki kwangilar sanya raga a titunan birnin Sakkwato da gwamnati ta bayar kan naira biliyan 30.
Jam’iyyar ta bayyana cewar, aikin asarar kudin jama’a ne domin ba ya da tasiri ga rayuwar al’umma, don haka, ta bukaci binciken gaggawa kan yadda gwamnatin Sakkwato ke kashe kudaden al’umma.
- Mene Ne Dalilin Da Ya Sa Kamfanonin Waje Su Zuba Jari Ga Kasar Sin?
- ‘Yan Nijeriya Na Cikin Matsi Saboda Hauhawar Farashin Kayayyaki – Abdulsalami
A jawabin da jam’iyyar ta fitar a ranar Laraba wanda kakakinta, Hassan Sahabi Sanyinnawal ya sanyawa hannu, jam’iyyar ta bayyana cewa, a shirye take ta fuskanci ko wane irin bincike kan ayyukan da gwamnatin Tambuwal ta aiwatar.
Jam’iyyar ta bayyana cewa, a shirye tsohon Gwamnan, da ‘yan majalisar zartaswarsa da manyan jami’an gwamnatinsa suke, su bayyana a gaban hukumar binciken a duk lokacin da aka bukata.
Kiran EFCC da ICPC su gudanar da binciken, ya biyo baya ne a yayin da gwamnatin jihar ta gabatar da takardar korafi ga hukumar da ta kafa kwamitiin binciken tsohuwar gwamnatin jihar kan zargin karkatar da hannun jari na naira biliyan 16 da gwamnatin Tambuwal ta yi.
A sanarwar, jam’iyyar ta zargi gwamna Ahmed Aliyu da almubbazaranci ta hanyar kashe biilyoyin kudade a ayyukan da ba su da muhimmanci kamar zagaye tituna da waya a daidai lokacin da jama’a ke cikin halin kunci da tsadar rayuwa.
Haka ma jam’iyyar ta bayyana cewa, a yayin da al’ummar jihar ke cike da mamaki da kaduwa kan kwangilar gyaran rijiyoyin burtsatse 25 kan naira biliyan 1.2 sai ga batun naira biliyan 30 na zagaya tituna da raga.
Jawabin ya ce, gwamnatin jihar ta na kokarin karkatar da hankalin jama’a ne kan gazawar gwamnatinsu ta hanyar zarge- zargen da ba su da tushe ga gwamnatin Tambuwal wanda jam’iyyar ta bayyana cewa, gwamnati ce mafi aiwatar da gaskiya da adalci wadda cibiyoyin bin diddigin ayyukan gwamnati na duniya suka tabbatar.
“Ayyukan gyaran sha-tale-tale da hanyoyin ratsewa da gwamnati ta bayar, ba a bi ka’idojin bayar da kwangila ba, domin an bayar da aikin ba tare da amincewar majalisar zartaswar gwamnati ba, ba kuma tare da cike ka’idoji ba.”
“A kan wannan, muna kira ga hukumomin EFCC da ICPC da su gudanar da cikakken bincike kan kwangilar biliyan 30 ta zagaya tituna da raga domin tabbatar da gaskiya da adalci ga al’ummar jihar Sakkwato.” In ji Jam’iyyar