Daga shekara sha biyar zuwa yanzu, Rabi’u Kwankwaso ya zama dan siyasa mafi kwarjini da farin jini a Kano, bayan Limamin canji; Dakta Abubakar Rimi ya kwanta dama. Kwankwaso, ba ma kawai batun kwarjini kadai ba; ya samu tasiri na mabiya a kungiyance, wadanda a koda-yaushe a shirye suke wajen amsa kiransa da zarar ya yi.
Yanzu kuma ga shi ya tsinci kansa a wani yanayi, wanda lokaci ne kadai zai iya tabbatar da ci gaban tasirinsa a sha’anin siyasa. Har ila yau, hukuncin babbar kotun koli, wanda ke wakana a halin yanzu tsakanin Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP tare da abokin hamayyarsa Nasiru Yusuf Gawuna, na Jam’iyyar APC ne kadai zai iya tabbatar da ci gaban haskawar tauraron Kwankwason ko disashewarsa.
- CAC Ta Bayyana Dalilan Da Ke Kawo Durkushewar Kamfanoni A Nijeriya
- 2023: Duk Da Matsalolin Tattalin Arziki, Bangaren Inshora Da Hannun Jari Sun Bunkasa
Wanda ke inuwar Kwankwason Abba Yusuf, bai samu nasara a shari’ar kotun sauraren korafe-korafen zabe ba, haka nan a kotu daukaka kara, inda Gawuna ya kalubalanci nasarar da ya samu a bangarori guda uku: 1) Cewa Abba Yusif ba dan jam’iyyar NNPP ba ne; 2) kuri’u 165,663 cikin kuri’u 1,019,602 da Jam’iyyar NNPP ta samu, ba halastattu ba ne; dalili kuwa ba sa dauke da sitamfi da sa-hannu. Saboda haka, rage yawan wadannan kuri’u zuwa 853, 939, shi ne 3) Ya bai wa Gawuna damar samun kuri’u 890, 705 da tazara ta 36,000, don haka a ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.
Saboda haka, kotu sauraren kararrakin zabe ta amince da wannan bukata, ta kuma yi hukunci a kai a wani boyayyen wuri wanda ba a bayyana ba, ta hanyar yanar gizo; wanda hakan ya haifar da cece-kuce tare da yin zanga-zanga a fadin jihar. Haka zalika, wani daga cikin ma’aikatan kotun ya shelanta cewa, wasu sun yi kokarin ganin Alkaliyar kotun, domin ba ta wasu makudan kudi a matsayin kyauta a boye, amma a karshe bangaren shari’ar ya musanta dukkanin wadannan zarge-zarge. Don haka, yanzu kacokan kallo ya koma kan kotun koli baki-daya.
Kotunan Nijeriya yanzu sun zama wata matattarar korafe-korafen zabe, domin kuwa an mayar da wuraren wajen shigar da kararrakin zabe, inda yanzu suke yin yanayi da wasu masana’antu da ke samun bunkasa da ci gaba cikin sauri. Masu zabe da zabe; kotu da bayyana wanda ya lashe zaben.
Abin da ba a saba gani ba
Duk da dimbin kararkin zaben da aka yanke shekaru a 20 da suka gabata, kadan ne wadanda a cikinsu kotunan kasa suka yanke hukunci kotun koli kuma ta warware. Saboda haka, batun karar zaben kujerar gwamna, yana tikewa ne a kotun daukaka kara. Sai daga baya aka yi wa dokar kwaskwarima ake danganawa ga kotun koli, inda aka bai wa kananan kutunan damar yanke nasu hukuncin, kafin a dangana ga kotun koli wadda ta kasance a matsayin raba gardama.
Daga abin day a faru da shari’ar Rotimi Amaechi da Celestin Omehia a shekarar 2007, a shari’ar da aka yi a shekarar 2016; inda kotun koli ta warware hukuncin kananan kotunan ta ayyana Nyesom Wike a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan Jihar Ribas (ba tare da bayyana dalilin aiwatar da hukuncin ba), haka nan abubuwa guda uku zuwa hudu da suka faru mafi ban mamaki sun hada da shari’ar da aka yi a shekarar 2019, wanda ya hada na Gwamnan Jihar Imo Hope Uzodimma.
Baya ga Reverend Ejike Mbaka wanda kyautarsa ta ban mamaki ta ba shi damar hango batun Uzodimma a jawabin da ya shahara da shi na “Ina ganin kwarin gwiwa ko fata”, mutanen da suka san me suke yi, ba za su iya fahimtar yadda mutumin da ya zo na hudu a zabe kuma zai dawo na farko ba. Kuma duk da haka, a wani hukunci da Kotun Koli ta yanke da ta soke na kananan kotuna, kotun ta ce Uzodimma ne ya lashe zaben.
Fata kuma?
A bayyane yake Kwankwaso da magoya bayansa na fatan ganin sun samu nasara, wanda a kowane hali, watakila ba su kai na Uzodimma ba. Amma ga dukkan alamu masu goyon bayan Gawuna sun kara matsawa gaba don samun damar da suke da ita a bangaren shari’a a halin yanzu. A shafin Wikipedia na jihar, alal misali, wasu mutane sun soke wa’adin Yusuf a watan Nuwamba lokacin da Kotun Daukaka Kara ta yanke hukuncinta. An bayyana Gawuna a wannan shafin a matsayin “gwamna mai ci” daga watan Nuwamba!
Kwankwaso ya sha yake-yake da dama amma wannan yakin na iya sake fasalta sauran kwanakin siyasarsa, da na tafiyar Kwankwasiyya. Babban kaye na farko da ya sha shi ne na shekaru 20 da suka gabata, lokacin da ya fadi zaben neman wa’adinsa na biyu a matsayin gwamna. A lokacin da guguwar kafa shari’ar musulunci ta mamaye Arewa, Kwankwaso ya mayar da kansa a matsayin mai matsakaicin ra’ayi.
Abokin hamayyarsa, Ibrahim Shekarau, ya yi abubuwa guda biyu: ya makale a tawagar Muhammadu Buhari, a karkashin tutar jam’iyyar ANPP; kuma mafi mahimmanci, shi ma ya bi sawun kafa shari’a. Ya yi babbar nasara, ba wai kawai ya kawar da Kwankwaso ba, har ma ya zama gwamna na farko a Kano da ya yi wa’adi sau biyu.
Shekarau ya doke dan takarar Kwankwaso, Aliyu Sani-Madawakingini, a takarar kujerar sanata a 2019, bayan wa’adin farko na Sanata. Jagoran tafiyar Kwankwasiyya dai ya sha kaye a zaben fidda gwani na takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, amma a yayin da ake tunkarar zaben 2019 sai ya sake komawa PDP. Idan za a iya tunawa, a lokacin zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC a 2015, Kwankwaso ya kasance dan takarar da jagoran jam’iyyar APC na kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya fi so a lokacin, kafin wata kakkarfar tawagar ‘yan Arewa ta matsa kaimi a kan takarar Buhari.
Shekarau ya yi amfani da tarin magoya bayan Buhari, inda ya karya lagon tafiyar Kwankwasiyya saboda jan daga da (Kwankwason) ya yi wajen kalubalantar farin jinin Buhari a Kano.
Sabon Kwankwaso
Sai dai Kwankwaso ya gawurta tun daga lokacin, musamman bayan cikar wa’adinsa na biyu na gwamna, wanda a lokacin ya samu karbuwa sosai saboda mayar da hankali a kan fannin ilimi da lafiya da kuma ababen more rayuwa. Har ila yau, ya yi amfani da matsayin da Kano take da shi na zama babban bankin samun yawan kuri’a a Nijeriya, ya taka muhimmiyar rawa, tare da wasu gwamnoni hudu na jam’iyyar PDP a 2015, wanda ya kai ga faduwar gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan.
Watakila babban abin da ke nuna gawurtarsa a siyasance shi ne kafa jam’iyyar NNPP ‘yan watanni kadan kafin zabukan da ya gabata, amma duk da haka jiha daya tak ya lashe – wacce ta fi kowace jiha a yankin Arewa maso Yamma – kuma ya zo na hudu a zaben da jam’iyyun siyasa 18 suka fafata. A yanzu dai wannan ginin da ya yi na fuskantar barazana.
Idan a baya Shekarau ne ya zama masa cikas, a shekaru takwas da suka wuce kuma tsohon mataimakinsa kuma shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Ganduje ne. A fafatawar da aka yi a Kotun Koli, Yusuf da Gawuna, a wani kaulin kamar ‘yan baranda ne. Wadanda suke fafata wasan su ne Kwankwaso da Ganduje.
Bayan zabukan da suka gabata, Kwankwaso ya yi kamar mai hazaka. A zahiri kamar dai ya samu wa’adi na uku a Kano kuma shugaba Tinubu, wanda ya lashe zaben shugaban kasa ya bukaci su tafi tare. Ba wai kawai don ya tabbatar da kansa a cikin wadanda tauraruwarsa ke haskawa ba, har ma dai duk wanda ke da iko a kan Kano dole ne a dama da shi a siyasa ta gaba.
Bayan zabe, yayin da Ganduje ke ci gaba da neman madafa ta biyu, shi Kwankwaso ya riga ya yi shigar sauri a wurin Tinubu. Ya gudanar da tarurruka da dama tare da shugaban kasar a cikin kasar da kuma a birnin Paris don rawar da zai taka a sabuwar gwamnati. An gaya mini cewa, a gaskiya, an dauke shi a matsayin wanda za a nada a ma’aikatar ilimi ko Birnin Tarayya Abuja.
Ganduje ya labe
Ganduje da wasu jiga-jigan ‘yan siyasa na kusa da Tinubu sun firgita. Amma Ganduje, mutumin da ake ganin ba zai iya cutar da ko da kuda ba, amma kuma sai ga shi yana farautar zaki, sai ya jira lokacin da zai yi uwar watsi. Da aka nada shi a matsayin shugaban jam’iyyar APC, duk da Kwankwaso, sai ya yi ja da baya irin na rago tare da kai karo shi da wasu ‘yan cikin gida wadanda su ma ba su ji dadin alakar da ake yi da Kwankwaso ba.
Ganduje ya kuma kara dagewa wajen tabbatar da duga-duginsa a wurin shugaban kasa bayan Gawuna ya yi nasara a kotun kararrakin zabe. Sannan Kwankwaso ko don takaici ko rashin yarda ya yi abin da zai iya zama babban kuskure. Ya yi ganawar sirri da Atiku a Abuja inda ya bar ‘yan jaridu da ‘yan siyasa suna yayyafa fetur a cikin wuta ta hanyar yin hasashe daban-daban kan kan dalilin ganarwa.
Yakin dai a yanzu ya shiga mataki na karshe. Idan da Kotun Koli za ta yi watsi da abin da ake ganin an karkata a kai kuma ta yanke hukuncin da zai bai wa Yusuf nasara, da Kwankwaso zai iya amfani da damar shari’a wajen wajen fatattakar Shekarau da Ganduje, manyan abokan hamayyarsa da dadewa. Idan kuma, kotun koli ta amince da hukuncin da kananan kotuna suka yanke, to kuwa Kwankwaso zai fara samun koma-baya ba tare da wata-wata ba.
Ayyana zaben a matsayin wanda bai kamala ba, ba zai yuwu ba. Amma wa ya sani?