Haramtacciyar kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biyafra (IPOB) ta gargadi tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso da ya daina alakanta kungiyar da burin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi.
Kakakin kungiyar ta IPOB, Emma Powerful ne ya bayyana hakan a lokacin da yake mayar da martani ga kalaman Kwankwaso na cewa ‘Yan Arewa ba za su zabi Obi ba saboda kin ‘yan Arewa da IPOB ke yi a yankin Kudu maso Gabas.
Kwankwaso ya yi furucin ne lokacin da ya bayyana acikin wani shirin Siyasa na tashar Talabijin ta Channels da akeyi ranar Lahadi.
Sai dai da yake mayar da martani ga ikirarin na Kwankwaso, kakakin haramtacciyar kungiyar IPOB, ya ce bai kamata a alakanta Obi da kungiyar ba, inda ya kara da cewa shi (Obi) bai yi shuhura ta dalilin kungiyar IPOB ba.