Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da nuna son kai ga yankin Kudu wajen rabon arzikin ƙasa, tare da ake watsi da yankin Arewa.
Kwankwaso ya bayyana haka ne a yayin taron tattaunawa da gwamnatin Kano ta shirya a dakin taro na gidan gwamnatin Kano a taron gyaran kundin tsarin mulki na 2025.
- Kwankwaso Ne Kaɗai Ɗan Siyasar Da Zai Iya Maye Gurbin Buhari — Jigo A NNPP
- Kwankwaso Ba Zai Sake Yi Mana Takarar Shugabancin Ƙasa Ba A Zaɓen 2027 Ba – NNPP
Taron ya samu halartar Gwamna Abba Kabir Yusuf da wakilan majalisun tarayya da na jiha, sai kuma sarakuna da shugabannin hukumomi da ƙungiyoyin farar hula da sauran masu ruwa da tsaki.
Kwankwaso, wanda ya taba zama gwamnan Kano sau biyu da kuma Ministan Tsaro, ya koka kan yadda ake ware Arewa a rabon kasafin kuɗi.
“Daga bayanan da muke da su, mafi yawan kasafin kuɗi yanzu yana tafiya ne zuwa ɓangare ɗaya kawai,” in ji shi. “Ina ba da shawara ga waɗanda suke son kwashe komai su tuna cewa matsalolin da muke fuskanta a Arewa da suka haɗa da tsaro da talauci yana da alaƙa da ƙarancin arziki da rashin kyakkyawan shugabanci.”
Ya ce tituna a Arewa sun lalace kuma gwamnati tana nuna rashin kulawa ga yankin. “Jiya da jirgi zan biyo na taho, amma aka ɗage jirgi daga ƙarfe 3 na yamma zuwa 8 na dare, sai na taho ta mota. Daga Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano abin takaici ne. Wannan aikin titi tun lokacin farkon hawa gwamnatin APC ake yinsa.”
Kwankwaso ya kara da cewa ana gudanar da manyan ayyuka a Kudu cikin hanzari, amma an bar ayyuka masu mahimmanci a Arewa babu kulawa.
“Muna jin ana gina titi daga Kudu zuwa Gabas. Muna maraba da ci gaba a ko’ina a Nijeriya. Amma gwamnati tana ɗaukar duk arzikin ƙasa ta zuba a ɓangare ɗaya kaɗai, ba ta yin aiki da ra’ayin ‘yan ƙasa gaba ɗaya,” cewarKwankwaso.
Ya roƙi gwamnatin Tinubu da ta sake duba tsarin rabon arziki tare da tabbatar da yin adalci a dukkan yankuna.
“Lokaci ya yi da gwamnati za ta sauya, ta tabbatar wa da ’yan Nijeriya cewa gwamnati ce ta ƙasa gaba ɗaya, ba ta wani ɓangare kawai ba,” in ji Kwankwaso.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp