Babban Kwanturolan Hukumar Shige da Fice ta Kasa, Isah Jere Idris, ya amince da nadin Tony Akuneme, mataimakin Kwanturolan Shige da Fice (DCI), a matsayin sabon kakakin hukumar.
Nadin nasa na dauke ne cikin wata sanarwa da kakakin sashen ayyuka, CSI KS Kure, ya fitar a ranar Laraba.
- Subul Da Bakan Tinubu: Alamu Ne Na Ba Zai Iya Shugabancin Nijeriya Ba- Dino Melaye
- Kotu Ta Kori Karar Da Maina Ya Shigar Kan Ministan Harkokin Cikin Gida Da Wasu
Ya maye gurbin DCI Amos Okpu wanda ya yi ritaya bayan shafe shekaru 35 yana yi wa kasa hidima.
DCI Akuneme, dan asalin Jihar Imo ne. Ya yi Digirinsa na farko a Falsafa a Jami’ar Fatakwal, da ke Jihar Ribas.
Ya kuma yi digirin digirgir a fannin shari’a na kasa da kasa a Jami’ar Legas da Difloma a aikin jarida.
Ya halarci kwasa-kwasai daban-daban a ciki da wajen kasar nan; ciki har da babban kwas na Sufiritanda a makarantar horon shige da fice da ke Kano.
DCI Akuneme ya yi aiki da sashen hulda da jama’a na NIS na tsawon shekaru 29 a fannin tsaron kan iyaka da gudanarwa.
A tsawon shekarun aikinsa a NIS, ya yi aiki a fannoni daban-daban.
Ya yi aiki tukuru a sashen kula da jama’ar, a 2015 ya yi aiki a ofishin karamin ministan Ilimi a matsayin Mataimaki na Musamman akan Yada Labarai har zuwa 2019.
A baya ya yi ayyuka daban-daban a gida da wajen kasar nan.
Ya kasance mataimakin kakakin shiyyar A, da ke Legas daga 1995 zuwa 2005, kakakin hukumar a Jihar Akwa Ibom daga 2005 zuwa 2008, mataimakin kakaki daga 2008 zuwa 2011 sannan ya rike mukamin babban jami’i a ofishin jakadancin Nijeriya da ke Kasar Kanada daga 2011 zuwa 2014.
Har zuwa lokacin nadinsa a baya-bayan nan, ya kasance Shugaban sashen hukumar da ke kula da ayyukan ‘yan Nijeriya da ke kasashen waje.
Tuni DCI Akuneme ya kama aiki a matsayin sabon kakakin Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya.