Kwanturolan Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), a Jihar Ribas, James Sunday, ya yaba wa ‘yan jarida bisa yadda suke yada ayyukan da hukumar take gudanarwa a cikin kasa da waje.
Kwanturolan wanda ya kasance tsohon jami’in hulda da jama’a na hukumar ya ce a matsayin ‘yan jarida na abokan aiki tare da kawo ci gaba, wajibi ne ya taya su murnar bikin ranarsu wanda aka yi na bana a ranar Laraba 3 ga watan Mayun 2023.
Sanarwar da ta fito daga ofishin NIS na Jihar Ribas, ta ce Sunday James ya kuma yi jinjina a kan yadda ‘yan jarida ke wayar da kan jama’a domin su fahimci hakkokinsu na kasa da kuma gudunmawar da ya kamata su bayar wajen gina kasa.
Ya kara da cewa, hukumar ta NIS a Jihar Ribas ta samu kwarin gwiwa wajen bayar da rahoton nasarorin da take samu tare da inganta ayyukanta da take gudanarwa domin ‘yan kasa.
Kwanturolan ya kuma yi amfani da wannan dama ta bikin ranar ‘yan jaridan wajen yaba wa Kwanturola Janar na NIS, Isa Jere Idris, MFR, saboda mutuntawa da hakurin da yake da shi da girmama ‘yancin ‘yan jarida da kuma jajircewarsa na yin aiki tare da kafafen yada labarai a matsayin abokan hadin gwiwa na kawo ci gaba.
Ya ba da misalin cewa, kasancewar Kwanturola Janar Jere, ya yi karatunsa na jami’a ne a fannin nazarin sadarwa, hakan ya kara kyautata alakarsa da ‘yan jarida wanda suke samun hadin kansa a duk lokacin da suka zo neman bayani ko Karin haske game da ayyukan da NIS take gudanarwa tun daga lokacin da ya kama aiki a matsayin shugaban hukumar.
Kwanturola James, ya ce ‘yan jarida na da kyakkyawar alaka, hadin gwiwa, da ‘yanci wajen samun bayanan da za su bukata ba tare da kawo cikas ga tsaron kasa daga NIS ba.
Ya kuma hori ‘yan jarida da su kasance masu adalci da kuma da’a ga aikinsu yayin da suke farauto labarai ko tattaunawa da jama’a domin ilmantar da ‘yan kasa. Kana ya hore su a koyaushe su yi kokarin inganta aikinsu tare da kawo sabon salo irin na ci gaban zamani, kana ya ba ta tabbacin NIS za ta ci gaba da kyautata alaka da ‘yan jarida a koyaushe a matsayinsu na abokan aiki.