Nasarar kasar Sin a fannin kwarewa, da ci gaban fasahar kere-kere ta zama abin koyi da ke ingiza burin zamanantar da aikin gona na Afirka, ta hanyar samar da ingantattun masana’antu, da bunkasa makamashi, da inganta albarkun bil Adam.
Darektan sashen raya harkokin noma da samar da ababen more rayuwa na hukumar raya masana’antu ta MDD wato UNIDO, Dejene Tezara ne ya shaidawa kamfani dillancin labarai na Xinhua hakan a kwanan baya, inda ya ce, cibiyar inganta harkokin masana’antu na Sin da Afirka da UNIDO da aka kaddamar a watan Nuwamba na shekarar 2024 a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, ta kasance dandali mai amfani wajen ciyar da sha’anin samun ci gaba mai dorewa na nahiyar gaba, ta hanyar raya masana’antu, da zamanantar da aikin gona, da bunkasa fasahohi.
- Dantsoho Ya Nemi Masu Zuba Hannun Jari Da Su Ci Gajiyar Tsarin EPT Na NPA
- A Cikin Mako Daya An Yi Asarar Naira Biliyan 365 A Kasuwar Sayar Da Hannun Jari
Tezera ya bayyana cibiyar a matsayin shaidar habakar hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa, yana mai cewa, kasar Sin tana ba da gudummawar ilmi, fasaha da albarkatunta, wajen samun nasarar hadin gwiwa, yayin da Habasha ke ba da kayayyakin aiki, da samar da muhalli mai taimakawa wajen aiwatarwa, kuma UNIDO ta zama gada ta tabbatar da ba da taimakon da cibiyar ke bukata da gudanarwa.
Tezera ya kara da cewa, a tashin farko, cibiyar ta mayar da hankali ne kan kasar Habasha, da burin kafa rassan cibiyar a kasashen Afirka daban-daban, ta yadda za su ba da gudummawa ga ci gaba mai dorewa a nahiyar. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp