ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, November 12, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kwarin Tubalin Tattalin Arzikin Sin Yana Karawa Kamfanonin Waje Kwarin Gwiwar Zuba Jari

by CMG Hausa
3 years ago
Tattalin Arzikin Sin

Wani rahoton kafar yada labarai ta china Daily ta kasar Sin, ya ruwaito a yau Talata cewa, kamfanonin kasashen waje na kara imani da tattalin arzikin kasar Sin kuma sun karfafa kudurinsu na fadada zuba jari a kasar Sin.

Wannan baya rasa nasaba da ci gaban tattalin arziki da kasar ta samu cikin rabin farko na bana, inda ya karu da kaso 2.5. Wannan kuma na da alaka da tubali mai kwari da aka gina tattalin arzikin kasar a kai.

  • Kasar Sin Za Ta Inganta Manufofin Taimakawa Dukkan Bangarorin Tattalin Arziki

Yayin da ake fama bullar annobar COVID-19 da wasu matsalolin duniya, hakika kasar Sin ta yi namijin kokari wajen tabbatar da tattalin arzkinta ya bunkasa ta hanyar dabarunta na hangen nesa da kuma bude kofarta ga waje.

ADVERTISEMENT

Ko a baya-bayan nan, babban bankin kasar ya sanar da kudurinsa na daukar wasu manufofin kudi domin taimakawa dukkan bangarorin tattalin arziki.

Har kullum, kasar Sin bata kasa a gwiwa wajen samar da yanayi mai kyau na habakar tattalin arziki, ta hanyar taimakawa dukkan bangarori.

LABARAI MASU NASABA

Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam

Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa

Duk da irin bata mata suna da ake yi, karin kamfanonin waje na kara karfafa imaninsu da ita, saboda sun amince da manufofinta, haka kuma ta na kokarin samar musu da yanayi mai kyau da kara habaka bangarorin zuba jari.

Yadda kasar Sin ke jagorantar bangaren fasahohin zamani, ya kara jan hankalin ‘yan kasuwar kasashen ketare. A kullum duniya na sauyawa, don haka, tafiya da zamani ya zama dole muddun ana son samun ci gaba. Kuma kasar Sin ta samar da wannan yanayi inda take karfafa gwiwar kirkire kirkiren sabbin fasahohin zamani, bangaren da ya karawa tattalin arzikin kasar da ma ‘yan kasuwa kuzarin zuba jari.

Haka zalika, yayin da a ko ina a duniya ake fama da hauhawar farashin kayayyaki fiye da kima, wannan lamari a kasar Sin yana kan wani matsakaicin mataki, inda babban bankin kasar ya yi imanin cewa, matakin zai daidaita.

A gaskiya dabarun kasar Sin suna haifar da da mai ido, domin suna tallafawa al’ummar kasar da yan kasuwar kasashen ketare har ma da taimakwa bunkasar tattalin arzikin kasashen dake hadin gwiwa da ita da ma duniya baki daya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam
Daga Birnin Sin

Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam

November 11, 2025
Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa
Daga Birnin Sin

Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa

November 11, 2025
CIIE Ya Kasance Gadar Sada Tattalin Arzikin Kasar Sin Da Na Duniya
Daga Birnin Sin

CIIE Ya Kasance Gadar Sada Tattalin Arzikin Kasar Sin Da Na Duniya

November 11, 2025
Next Post
Yawan Tashar Sadarwa Ta 5G Da Sin Ta Gina Ya Kai Kusan Miliyan 2

Yawan Tashar Sadarwa Ta 5G Da Sin Ta Gina Ya Kai Kusan Miliyan 2

LABARAI MASU NASABA

Coas

Bayan Ganawa Da Tinubu, COAS Ya Tabbatar Wa ‘Yan Nijeriya Samun Ingantaccen Tsaro

November 11, 2025
Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam

Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam

November 11, 2025
Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa

Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa

November 11, 2025
Za Mu Ci Gaba Da Tallafa Wa ’Yansanda Domin Inganta Ayyukan Su A Zamfara – Gwamna Lawal

Za Mu Ci Gaba Da Tallafa Wa ’Yansanda Domin Inganta Ayyukan Su A Zamfara – Gwamna Lawal

November 11, 2025
CIIE Ya Kasance Gadar Sada Tattalin Arzikin Kasar Sin Da Na Duniya

CIIE Ya Kasance Gadar Sada Tattalin Arzikin Kasar Sin Da Na Duniya

November 11, 2025
CMG Ya Gabatar Da Sabbin Manhajoji 10 Da Ya Kirkiro Don Watsa Gasar Wasannin Motsa Jiki Ta Kasar Sin Karo Na 15

CMG Ya Gabatar Da Sabbin Manhajoji 10 Da Ya Kirkiro Don Watsa Gasar Wasannin Motsa Jiki Ta Kasar Sin Karo Na 15

November 11, 2025
‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 3 A Nasarawa

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 3 A Nasarawa

November 11, 2025
Cikin Wata Ɗaya, ‘Yansanda Sun Kama Mutane 200 Da Ake Zargi Da Laifuka A Katsina

Cikin Wata Ɗaya, ‘Yansanda Sun Kama Mutane 200 Da Ake Zargi Da Laifuka A Katsina

November 11, 2025
CIIE Ya Ba ‘Yan Kasuwar Afirka Damar Habaka Cinikinsu Da Sin 

CIIE Ya Ba ‘Yan Kasuwar Afirka Damar Habaka Cinikinsu Da Sin 

November 11, 2025
Me Sabon Tarihin Da Aka Kafa A Baje Kolin CIIE Ke Nunawa?

Me Sabon Tarihin Da Aka Kafa A Baje Kolin CIIE Ke Nunawa?

November 11, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.