Shugaban Hukumar Kwastam, ta Kasa Kwastam, Adewale Adeniyi, ya jaddada mahimmancin yan hadaka a tsakanin Hukumarsa, da Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA, musamman domin Hukumomin biyu, su bunkaa inganci gudanar da aiki da kuma kara bunkasa yin gasar yin hada-hadar Kasuwanci, a Tashoshin Jiragen Ruwa na kasar.
Adewale ya bayyana haka ne, a yayin da ya kai ziyarar aiki a kwanan baya, a Hukumar ta NPA.
- An Bude Cibiyar Tattarawa Da Yada Labarai Ta Taruka Biyu Na Sin
- Gwamnatin Kano Za Ta Ɗau Nauyin Ɗalibai 1,002 Domin Karatu A Ƙasashen Waje
Ya yi nuni da cewa, nasarorin da Hukumar Kwatan ta kasa ta samu, kusan sun jibantu ne, kan yadda ake gudanar da ingantaccen ayyukan, tafiyar da Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar.
“Sai idan komai ta tafi daidai a Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar ne, kana komai zai tafi daidai, a Hukumar ta Kwastam ta Kasa.”
“Muna da dimbin shirye-shiyen da muke son wanzarwa a Kwastam wanda hakan ya sanya, dole muke bukatar yin hadaka da sauran masu ruwa da tsaki, kamar da Hukumar ta NPA, musamman domin wadannan dimbin shirye-shiyen da muke son wanzarwa, su samu kai wag a nasara.”
Shugaban ya kuma yaba da hadar da tuni Hukumarsa ke kan ci gaba da yi da NPA ta kan kayan da ake fitarwa da su zuwa ketare, da ke a gabar ruwa ta Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar.
A na sa jawabin Shugaban Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA, Dakta Abubakar Dantsoho, ya bai wa Shugaban na Hukumar Kwastam tabbacin goyon baya da hadin kan NPA, domin Hukumomin biyu, su samu cin nasarar abinda suka sanya a gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp