Hukumar kwastam ta kama makamai da harsasai da aka yi yunkurin shigowa da su Nijeriya, ta tashar ruwan Onne da ke Jihar Ribas.
Da yake ba da sanarwar a ranar Litinin yayin taron manema labarai, shugaban hukumar Adewale Adeniyi ya ce dakarun hukumar sun yi nasarar kama makaman ne tun ranar 21 ga watan Yuni.
- Wata Sabuwa: KEDCO Ta Yanke Wutar Jami’ar Dangote Da Ke KanoÂ
- Matukin Jirgin Sojin Saman Nijeriya Ya Tsallake Rijiya Da Baya
Ya ce, bayan tattara bayanan sirri, dakarun sun lura da wata kwantena da ta fito daga kasar Turkiyya wadda ke dauke da bindigu 844 da kuma kunshi harsashi 112,500.
“An kunshe su ne a cikin kofofi, da kayan daki, da kayan gyaran famfo, da jakunkunan leda, wadanda aka biya wa kudin haraji na Naira miliyan ₦4,171,710,000.00,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa, a ranar Lahadi ma dakarun kwastam sun tare wasu kwantena takwas masu tsawon kafa 40 da aka yi niyyar kai wa wani wurin ajiya daga tashar ta Onne.
“Suna dauke ne da kwalaben maganin tari 1,050,000, da kwayoyin Trodol Benzhexol 3,500,000, da dilar kayan gwanjo 720 da aka biya wa harajin naira miliyan ₦13,915,710,000.00.,” a cewarsa.