Hukumar Kwastam a jihar Adamawa, ta kama fatun Jakuna 200 da aka yi fasakwaurin su a cikin wata mota da cafke wasu kaya da kudinsu ya kai naira miliyan 1.9 a jihar.
Shugaban hukumar na yankin, Salihu Kazaure, ne ya bayyana hakan ranar Alhamis a wani taron manema labarai a garin Yola.
- Hadarin Kwale-Kwale Ya Sake Yin Sanadiyyar Mutuwar Fasinjoji 11, 10 Sun Bace A Adamawa
- Mutum 15 Sun Rasu, 8 Sun Bace A Hatsarin Kwale-Kwale A Adamawa
Kazaure ya ce, masu fasa kaurin sun gudu sun kutsa cikin wani daji sun bar kayan a wani kauye da ke iyakar kasar Kamaru.
A wani labarin makamancin wannan, Jami’an hukumar a watan Satumbar da muke ciki na shekarar 2023, sun yi nasarar kwace buhunan Shinkafa ‘yar kasar waje guda 127 masu nauyin kilo 50 da litar mai samfarin guda 12,350.
Hukumar ta ce, masu kai wa masu fasa kaurin bayanan sirri a wasu yankuna su ne babban kalubalen da hukumar ke fuskanta a gudanar da ayyukanta.
Hukumar ta shirya tsab don hada hannu da masu rike da sarautun gargajiya da ‘yan jarida don wayarwa da jama’a kai kan irin kayan da gwamntin tarayya ta haramta shigo wa da su zuwa cikin gida Nijeriya.