Kwanturolan hukumar kwastam (NCS), Adewale Adeniyi, a ranar Talata, ya sanar da kama wasu jiragen sama marasa matuka, jabun kayayyaki, magunguna, da kuma wadanda wa’adin aiki da su ya cika a tashar jirgin ruwa ta Apapa da ke Legas.
Kayayyakin da aka kama, an kimanta darajarsu ta haura sama da Naira biliyan 921.
- Gwamnan Sokoto Ya Amince Da Sauya Wa Manyan Sakatarori 25 Ma’aikatu A Jihar
- Xi Ya Jaddada Muhimmancin Tsara Nagartaccen Shirin Raya Tattalin Arziki Da Zamantakewar Al’umma Tsakanin 2026-2030
Adeniyi ya bayyana hakan ne a taron manema labarai, inda ya ce an kama kayayyakin ne a tsakanin watan Janairu zuwa Afrilun 2025, yana mai cewa, jirage marasa matuka da ake amfani da su wajen tsaro ba su da takaddun shaida daga ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro (ONSA) na kasa.
Ya bayyana cewa, ziyarar da ya kai a tashar ruwa ta PTML da Tin Can na da nufin sanin irin kalubalen da jami’an sa ke fuskanta wurin amfani da sabuwar na’urar zamani domin binciken kayayyakin da ake shigowa da su kasar.
Ya kuma kara gargadin jama’a game da karuwar kwararowar magunguna kasar da ba su da rajista, musamman magungunan inganta jima’i, inda ya yi gargadin cewa irin wadannan abubuwa na da matukar barazana ga kiwon lafiyar jama’a.
Ya yi gargadin cewa, yin amfani da wadannan magungunan ba tare da kulawar likitoci ba zai iya haifar da mummunar illa ga lafiyar jiki, ciki har da haɗarin cututtukan zuciya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp