Hukumar Hana Fasa Kwauri ta Kasa (NCS), ta kame kayayyakin sama da naira miliyan 55 a cikin kasa da mako biyu a Jihar Adamawa.
Da ya mke yi wa ‘yan jarida bayani a Yola, shugaban hukumar a jihihohin Adamawa da Taraba, Suleiman Abdullahi, ya ce baya ga kayayyakin hukumar ta kuma cafke litar man fetur 34,850, da ake yunkurin shiga kasar Kamaru, hukumar ta kwace.
- Bikin Canton Fair Ya Samar Da Dimbin Damammakin Kasuwanci
- Buhari Ya Bukaci Majalisa Ta Tabbatar Da Nadin Mambobin Majalisar NEDC 12
Shugaban hukumar ya ce hukumar na aiki da bangarorin jami’an tsaro a jihar da nufin kawo karshen shigo da kayayyaki ta haramtattun hanya dama shigo da kayayyakin.
Ya ce, “Tun daga ranar 18/4/2023, da na zo jihar a matsayin shugaban hukumar NCS, hukumar ta cimma nasarori dama, wadanda suka kara karsashin hukumar kwastom da jami’anta.
“Hukumar NCS a jihohin Adamawa/Taraba, haka kuma da sauran jihohin da ke kan iyakokin arewa sun kwashe shekaru kan iyakokinsu a rufe, amma abin bakin ciki wasu gurbatattun mutane su na bin wasu hanyoyi su shigo ko fita da kayayyaki.
“Ina gargadi ga duk jami’anmu da su tashi tsaye su kiyaye aikin da aka dora musu, mun ba je komarmu, domin cafke masu shigo fita ko shigo da kayayyaki a jihar nan” inji Suleiman.
Cikin kayayyakin da hukumar ta cafke har da takin NPK, da shugaban hukumar ya ce an dakatar da shigo da shi musamman a jihohin arewacin Nijeriya.