A ranar Laraba ne Hukumar Kwastam da ke aiki a filin jirgin sama na Murtala Muhammed (MMA) da ke Legos ta ce ta kama fakiti 23 na kwayar tramadol da darajarsu ta kai Naira biliyan 1.8 da aka shigo da su cikin Nijeriya daga Indiya da Pakistan.
Da yake jawabi yayin wani taron manema labarai a filin jirgin sama na Legas kan ayyukan rundunar a rubu’in farko na shekara, kwamandan kwastam (CAC) na hukumar, Compt. Mohammed Yusuf, ya ce tramadol din da aka kama ta wuce adadin wacce doka ta amince a shigo da ita kasar.
Kwanturola Yusuf, ya bayyana cewa za a mika kwayar da aka kama ga hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA domin ci gaba da bincike.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp