Hukumar kwastam ta shiyya ta daya ta kwace tire-la 13 da aka makare da shinkafar waje, da motoci 17, da sauran wasu kaya da suka kai Naira bilyan 1,241,777,700, a watan Oktoba, 2023.
Mai rikon mukamin Kwanturola na shiyyar, Hussein Ejibunu, ya bayyana wa manema labarai hakan a hedikwatar shiyyar da ke Legas.
- Kwastam Ta Kama Fatun Jakuna Da Aka Yi Fasa Kwaurinsu A Jihar Adamawa
- Gwamnatin Tarayya Ta Yi Fatali Da Zargin Da Obi Ya Yi Mata Kan Karin Kasafin Kuɗi
Ejibunu ya yi bayanin cewa an kwace motocin 17 ne daga wurin masu fasa-kwauri (‘yan sumogal), inda ya kara da cewa shiyya ta daya da take karkashin ku-lawarsa za ta hana masu sumogal cin karensu ba babbaka a sauran kwanakin da suka rage cikin wan-nan shekarar.
“Sauran kayan da aka kwace a watan sun hada da li-tar mai 14,825, tsofaffin tayoyi 657, tabar wiwi kilo-giram 20, dila 39 na kayan gwanjo, fakiti 100 na tu-matari, mashin 4, katon 100 na sabulun da aka yi amfani da shi, da buhu 730 na kirgi da fata”, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Jami’in ya bayyana cewa an kama mutane 9 lokacin da aka kai samamen na hana fasa -kwauri, wasu daga cikinsu ana bincike a kansu a jihohin da suke karkashin shiyyar.