Hukumar Kwastam ta Nijeriya, Sashin Ayyuka na Tarayya, Zone ‘D’ ta kama haramtattun kayayyaki da kudin ya kai Naira biliyan 1.17 tsakanin 30 ga Janairu zuwa 9 ga Agusta, 2023.
Mukaddashin Konturola na FOU Joseph Adelaja ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Bauchi.
Adelaja ya ce, a lokacin da ake gudanar da bincike, rundunar ta kama jimillar mutum 88, daga ciki akwai lita 174,585 na albarkatun mai da buhu auna na sikelin pangolin da kwayoyi da nauyinsu ya kai kilogiram 396.4.
Sauran a cewarsa, buhu 1,800 na sukari mai nauyin kilo giram 50 kowanne, sai kuma buhunan taki 343 da buhunan shinkafa 328 na kasar waje mai nauyin kilogiram 50 da dai sauransu.
“Rundunar ta kuma kama buhu tara na sikelin pangolin da kwayoyi masu nauyin kilo girma 396.4.
“Wasu kuma tsuntsaye ne masu rai guda biyu (Krane mai kambi na Afirka), sai barewa daya mai rai, kashin zaki daya da kuma kwandon kitsen zaki a roba,” in ji shi.
Adelaja ya kara da cewa, jami’an sun kama katan 88 na maganin kashe kwari, fakiti 342 na alewa ta waje, katan 190 na kayan shaye-shaye masu dadin dandano, buhunan takalmi 23 da aka yi amfani da su da buhunan sukari 1,800 kilo giramg 50 kowanne.