A yau Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira ga Sin da Korea ta Kudu da su daukaka dangantakarsu zuwa matsayi na gaba ta yadda al’ummominsu za su kara amfana da ita da kawo tabbaci ga duniya mai cike da rashin tabbas, yayin da yake taya Lee Jae-myung murnar lashe zaben shugabancin kasar.
Tabbas kyakkayawar alaka tsakanin Sin da Korea ta kudu ta dace da yanayin da duniya ke ciki da muradun al’ummomin kasashen da ma tabbatuwar zaman lafiya a yankinsu da ma duniya baki daya. A matsayinsu na makwabta, wadanda suka shafe shekaru 33 da kulla huldar diplomasiyya, kyakkyawar hulda tsakaninsu na da matukar muhimmanci musamman a irin wannan lokaci da duniya ke cike da hargitse da sauye-sauye da rashin tabbas.
Kamar yadda shugaba Xi ya bayyana, kasashen biyu makwabta ne da ba za a iya raba su ba. Don haka, ci gaban kowacce daga cikinsu, ci gaba ne ga dayar, haka ma akasinsa. Babu wanda yake kin cudanyar kasa da kasa, amma ya kamata, kowacce ’yantacciyar kasa ta kasance mai ra’ayinta na kashin kai da duba moriyarta da na makwabtanta yayin da take hulda da kasashen waje. Tarihi ya nuna yadda daidaituwar al’amura tsakanin bangarorin biyu ke samun tagomashi yayin da rashinsa ke haifar da koma baya. Yayin da Korea ta Kudu ta samu sabon shugaba, fatan ita ce zai jagoranci kasar wajen tsayawa kan ra’ayi na gaskiya da girmamawa da daidaito yayin cudanya da kasar Sin maimakon ba da dama ga masu wani ra’ayi na son kai don amfani da ita da zummar cimma burinsu. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp