Tawagar Super Falcons ta Nijeriya ta lashe kyautar tawagar kwallon mata mafi kwazo a Afirka a bikin bayar da kyautar CAF ta 2023 da aka yi a Morocco a daren Litinin.
Wannan kyautar ta biyo bayan rawar da tawagar suka taka a gasar cin kofin duniya ta mata ta ‘FIFA 2023’ a Australia da New Zealand.
Tawagar Super Falcons sun kai zagaye mai kasashe 16 a gasar kofin Duniya ta mata kafin kasar Ingila ta fitar dasu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp