Tun bayan fitar da jerin sunayen yan wasan kwallon kafar da ke takarar samun babbar kyutar zinare ta Ballon D’or ake ta muhawara akan shin Lionel Messi zai iya lashe kyautar Ballon d’Or karo na takwas?.
Ko kuma Erling Haaland wanda shi ma yana cikin fafatawa bayan da ya yi fice a kakar wasa ta farko da Manchester City.
An fitar da jerin sunayen ‘yan takara na Ballon d’Or na maza da mata.
An kuma bayyana sunayen wadanda aka zaba don kyautar Yashin da Kopa – wanda ake ba mafi kyawun mai tsaron gida da dan wasan kasa da shekara 21.
Yaushe ne Ballon D’or 2023?
Za a gudanar da bikin Ballon d’Or na 2023 a gidan wasan kwaikwayo na Chatelet a birnin Paris ranar 30 ga Oktoba.
Wannan shine lokacin da za a bayyana wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or 20232023.
Wanene Zai Iya Lashe Ballon D’or 2023?
Messi ne ya fi kowa damar lashe kyautar karo na takwas bayan da ya jagoranci Argentina zuwa gasar cin kofin duniya da aka yi a Qatar a watan Disamba.
Dan wasan mai shekaru 36 ya zura kwallaye bakwai, ciki har da biyu a wasan karshe, kuma ya lashe kyautar zinare bayan da ya nuna bajinta.