Gwamnan jihar Jigawa, Mallam Umar Namadi ya bayyana cewa karramawar da LEADERSHIP ta yi masa a ranar Talata za ta kara zaburar da shi da tawagarsa wajen jajircewa da sauke nauyin da ya rataya akan gwamnatinsa.
Gwamna Namadi ya bayyana hakan ne bayan ya karbi kyautar gwarzon gwamna na shekara, inda ya bayyana karramawar a matsayin “abin burgewa da girmamawa”.
- Sin Za Ta Mai Da Martani Kan Barazanar Kara Kakkaba Mata Harajin Kwastam Daga Amurka
- Hafsan Soji Ya Gana Da Shugabanni A Filato Kan Hare-haren Da Suka Yi Ajalin Mutane
Gwamnan ya kuma bayyana jin dadinsa da irin kyakkyawan hangen nesan da ya janyo aka shirya wannan gagarumin taron wanda ya samar da dandalin tattauna batutuwan kasa.
Ya jaddada cewa, taken taron ya dace kuma yazo a kan lokaci “wanda na yi imanin cewa, dandalin zai taimaka wajen gabatar da jawabai a bangarori daban-daban na gyare-gyaren kasafin kudi da shugaba Bola Tinubu ke aiwatarwa a karkashin shirin renewed hope.”
Ya ce, jawabin da ake gabatarwa a dandalin zai ba da gudummawa ga kudirin dokar gyaran haraji da ke gaban majalisar dokokin kasar don karfafa tsarin tarayyar Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp