• English
  • Business News
Friday, October 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kyautata Alakar Sin Da Amurka Na Iya Shawo Kan Matsalolin Duniya

by CMG Hausa
3 years ago
Sin

Yayin da taron koli na kungiyar G20 zai mayar da hankali wajen tattauna muhimman batutuwan da ke ciwa duniya tuwo a kwarya, kamar na tattalin arziki da wadatar abinci da makamashi da batun Ukraine da sauransu, ya samar da wata muhimmiyar dama ta tattaunawar keke da keke, tsakanin shugabannin manyan kasashen duniya biyu, wato Sin da Amurka.

Karon farko tun bayan hawansa karagar mulkin Amurka, shugaba Joe Biden ya gana ido da ido da takwaransa na kasar Sin Xi Jinping a jiya, gabanin taron.

  • Xi Jinping: Sin Na Goyon Bayan Shigar Da Kungiyar AU G20

Hakika, wannan wata dama ce ta warware zare da abawa game da batutuwan dake haifar da tsamin dangantaka tsakanin manyan kasashen biyu.

Amurka ta dade tana takalar kasar Sin da gangan, yayin da a kullum, kasar Sin kan gargadi Amurkar tare da jan hankalinta game da muhimmancin girmama juna da hadin gwiwa a tsakaninsu.

Da alama za a samu saukin abubuwa, duba da yadda shugaban na Amurka ya nanata cewa, matsayar kasarsa ta kiyaye manufar Sin daya tak a duniya ba ta sauya ba, kuma ba ta son gogayya tsakaninsu ta rikide zuwa rikici. Gogayya ko Takara mai tsafta tsakanin manyan kasashen biyu mai, za ta iya zama mai amfanawa al’ummunsu da kuma duniya, muddun Amurka ba ta ci gaba da yin amai tana lashewa ba.

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Taya Kim Jong Un Murnar Cikar Jam’iyyar WPK Shekaru 80 Da Kafuwa

An Jinjinawa Tallafin Kamfanonin Sin Ga Tsarin Bunkasa Masana’antun Senegal

Kamata ya yi ta dauki shawarar kasar Sin, wato mutunta juna da girma cikakken ’yanci da moriyar juna, su kasance tushen huldar kasashen biyu. Kana akwai bukatar ’yan siyasar Amurka, su fahimta tare da kiyaye furucin na shugabansu, su dakatar da duk wani yunkurin lalata dangantaka a tsakanin kasashen biyu da neman haddasa rigima.

Kamar yadda shugaba Xi Jinping ya bayyana, a matsayinsu na shugabannin manyan kasashe biyu, ya kamata su lalubo hanyar da ta dace da kyautata dangantakarsu, domin yanayin da take ciki a yanzu, ba ta dace da moriyarsu da ma ta daukacin al’ummar duniya ba.

Ba shakka, kasashen duniya na mayar da hankalinsu ga irin yanayin da Sin da Amurka ke ciki. Kyautata alaka a tsakaninsu za ta iya magance sama da rabin batutuwan da duniya ke fuskanta.

Haka kuma, za ta kasance abun koyi ga kasashe masu tasowa. Ya kamata Amurka ta mara baya ga yunkurin Sin na tallafawa kasashe masu rauni da ma wadanda ke tasowa, maimakon ta rika yi mata zagon kasa ko neman bata mata suna. Sin ta yi an gani, kuma tana ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a duniya duk da tarin nauyin al’umma biliyan 1.4 dake wuyanta a cikin gida. Idan har da gaske Amurka na son kyautata dangantakarsu domin duniya baki daya ta amfana, ya kamata ta dakatar da rajinta na bata sunan kasar Sin da yada karairayi, ta rungumi hanyar zaman lafiya da bayar da gudunmawa ga kokarin Sin domin kai wa ga gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil adama. (Fa’iza Mustapha)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Xi Ya Taya Kim Jong Un Murnar Cikar Jam’iyyar WPK Shekaru 80 Da Kafuwa
Daga Birnin Sin

Xi Ya Taya Kim Jong Un Murnar Cikar Jam’iyyar WPK Shekaru 80 Da Kafuwa

October 10, 2025
An Jinjinawa Tallafin Kamfanonin Sin Ga Tsarin Bunkasa Masana’antun Senegal
Daga Birnin Sin

An Jinjinawa Tallafin Kamfanonin Sin Ga Tsarin Bunkasa Masana’antun Senegal

October 9, 2025
Masu Kallon Fina-Finai Na Sin Sun Gamsu Da Fina-Finan Da Aka Gabatar A Lokacin Hutun Bikin Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar Sin Ta 2025
Daga Birnin Sin

Masu Kallon Fina-Finai Na Sin Sun Gamsu Da Fina-Finan Da Aka Gabatar A Lokacin Hutun Bikin Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar Sin Ta 2025

October 9, 2025
Next Post
Sin

A Dauki Hakikakin Matakai Domin Kyautata Hulda A Tsakanin Sin Da Amurka

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Taya Kim Jong Un Murnar Cikar Jam’iyyar WPK Shekaru 80 Da Kafuwa

Xi Ya Taya Kim Jong Un Murnar Cikar Jam’iyyar WPK Shekaru 80 Da Kafuwa

October 10, 2025
An Zuba Jarin Dala Biliyan 5.2, An Sa Hannu Kan Yarjejeniyoyi 47 A Taron Tattalin Arziƙin Bauchi 

An Zuba Jarin Dala Biliyan 5.2, An Sa Hannu Kan Yarjejeniyoyi 47 A Taron Tattalin Arziƙin Bauchi 

October 10, 2025
Nijeriya

Haramcin Haƙar Ma’adanai: Majalisa Za Ta Kawo Ƙarshen Asarar Dala Biliyan 9 Duk Shekara

October 10, 2025
Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano

Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano

October 10, 2025
Yadda Rashin Isassun Malaman Turanci Da Lissafi Ke Shafar Ingancin Ilimi A Nijeriya (3)

Yadda Za A Magance Yawaitar Malaman Da Ba Su Cancanta Ba A Nijeriya – TRCN

October 10, 2025
Gwamnatin Katsina Ta Rufe Makarantu 32 Masu Zaman Kansu Da Ba Su Da Lasisi

Gwamnatin Katsina Ta Rufe Makarantu 32 Masu Zaman Kansu Da Ba Su Da Lasisi

October 10, 2025
Sin

Burin ‘Yan Nijeriya Bai Cika Ba Tun Bayan Samun ‘Yancin Kai

October 10, 2025
Matatar dangote

ACF Ta Yi Zargin Shiri Na Musamman Don Rusa Matatar Man Dangote

October 10, 2025
Yadda Zargin Takardar Karatun Bogi Ta Tilasta Wa Minista Nnaji Murabus

Yadda Zargin Takardar Karatun Bogi Ta Tilasta Wa Minista Nnaji Murabus

October 10, 2025
Gwamnatin Kogi Ta Yaba Wa Tinubu Kan Naɗin Amupitan Shugaban INEC

Gwamnatin Kogi Ta Yaba Wa Tinubu Kan Naɗin Amupitan Shugaban INEC

October 10, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.