• English
  • Business News
Tuesday, October 28, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kyautata Dangantaka Da Sin Na Iya Taimakawa Amurka Shawo Kan Matsalar Tattalin Arzikin

by CMG Hausa
3 years ago
Sin

Da safiyar yau Talata ne mataimakin firaministan Sin Liu He da sakatariyar baitulmalin Amurka Janet Yellen suka tattauna bisa gayyatar jami’ar ta Amurka. 

Cikin batutuwan da Jami’an biyu suka tattauna, akwai na samar da daidaito a fannin sarrafa hajoji da shigar da su kasuwanni da farfado da tattalin arzikin duniya.

  • Saudiyya Ta Kara Wa Maniyyatan Nijeriya Kwanakin Jigilar Alhazai

Dukkan kasashen biyu na da fasahohi da dabaru daban-daban da za su amfani juna. Kasar Sin a nata bangare, ta fi samar da kayayyaki masu rahusa, kana ta yi suna a duniya, wajen kerawa da sarrafa kayayyaki. A don haka, ’yan kasuwar Amurka za su iya amfana daga dimbin basirarta.

A nata bangare, Amurka za ta iya amfana da manufar bude kofa ta kasar Sin, har ma da babbar kasuwar da kasar ke da ita.

Sin ta sha nanata cewa kofarta a bude take ga ’yan kasuwar kasa da kasa, haka kuma a ko da yaushe, tana fadada bude kofar da rage yawan jerin bangarorin da kamfanonin waje ba za su iya zubawa jari ba, hakan ne ya sa ake ci gaba da ganin karuwar jarin kasashen waje a kasar. Haka kuma, bisa tubali mai karfi da tattalin arzikinta ke da shi, kamfanonin Amurka za su iya amfana sosai fiye ma da idan suka tsaya a kasarsu, muddun suka kiyaye dokoki da ka’idojin kasar Sin.

LABARAI MASU NASABA

Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Jama’a Ga Tsarin Jagoranci Na Sin

An Kusa Kammala Shirye-shiryen Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas

A matsayinsu na manyan kasashe, akwai dimbin abubuwan da za su iya amfana da su daga juna, muddin Amurka ta ajiye girman kai da cin zali. A halin yanzu, ana fuskantar hauhawar farashin kayayyaki da matsalar tattalin arziki mafi muni a Amurka, hadin gwiwa da koyon dabarun kasar Sin, za su taimaka mata wajen shawo kan matsalar.

Idan ba a manta ba, Amurka ce ta fara kakkaba haraji kan wasu kayyakin Sin dake shiga kasar da fakewa da manufar tsaron kasa wajen hana kamfanoninta mu’amala da wasu daga cikin kamfanonin Sin, har ma an ga yadda a baya-bayan nan, ta zartas da dokar da ta gindaya sharuda kan audugar jihar Xinjiang.

Sai dai dukkan wannan bai sa tattalin arzikin Sin ya durkushe ba, sai ma kara samun tagomashi. Wannan manuniya ce dake cewa, ya kamata Amurka ta yi karatun ta nutsu ta duba moriyarta da na al’ummarta, ta hada hannu da Sin domin a gudu tare a tsira tare domin amfanawa al’ummunsu da ma farfado da tattalin arzikin duniya baki daya. (Faeza Mustapha)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Jama’a Ga Tsarin Jagoranci Na Sin
Daga Birnin Sin

Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Jama’a Ga Tsarin Jagoranci Na Sin

October 28, 2025
An Kusa Kammala Shirye-shiryen Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas
Daga Birnin Sin

An Kusa Kammala Shirye-shiryen Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas

October 28, 2025
Fasahohin Sin Za Su Iya Kyautata Makomar Nahiyar Afrika
Daga Birnin Sin

Fasahohin Sin Za Su Iya Kyautata Makomar Nahiyar Afrika

October 28, 2025
Next Post
Ko Hukumar Kwastam Su Gyara Tsarin Dutin Motoci Ko Kuma A Daina Yi Gaba-daya —Majalisa

Ko Hukumar Kwastam Su Gyara Tsarin Dutin Motoci Ko Kuma A Daina Yi Gaba-daya —Majalisa

LABARAI MASU NASABA

Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Ajali Tare Da Jikkata Wasu A Gombe

Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Ajali Tare Da Jikkata Wasu A Gombe

October 28, 2025
Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Jama’a Ga Tsarin Jagoranci Na Sin

Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Jama’a Ga Tsarin Jagoranci Na Sin

October 28, 2025
Kano Ta Bai Wa Mata 5,200 Tallafin Naira Miliyan 260

Kano Ta Bai Wa Mata 5,200 Tallafin Naira Miliyan 260

October 28, 2025
An Kusa Kammala Shirye-shiryen Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas

An Kusa Kammala Shirye-shiryen Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas

October 28, 2025
Gwamna Bago Ya Amince Da Biyan Karin Albashin Naira 20,000 Ga Ma’aikata 

Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Hutun Kwanaki 2 Don Zaɓen Ƙananan Hukumomi

October 28, 2025
Fasahohin Sin Za Su Iya Kyautata Makomar Nahiyar Afrika

Fasahohin Sin Za Su Iya Kyautata Makomar Nahiyar Afrika

October 28, 2025
Xi Ya Yi Karin Haske Kan Muhimman Shawarwarin Da Kwamitin Kolin JKS Ya Gabatar Yayin Tsara Shirin Raya Kasa Karo Na 15

Xi Ya Yi Karin Haske Kan Muhimman Shawarwarin Da Kwamitin Kolin JKS Ya Gabatar Yayin Tsara Shirin Raya Kasa Karo Na 15

October 28, 2025
gaza

Majalisar Dattawa Ta Maido Da Ranar Tantance Sabbin Shugabannin Sojoji Zuwa Laraba

October 28, 2025
Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani

Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani

October 28, 2025
Ina Fatan Buga Kofin Duniya Na 2026 — Messi

Ina Fatan Buga Kofin Duniya Na 2026 — Messi

October 28, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.