Ana cewa, ba ka isa ka isar da Mutane ba da dukiyarka amma za ka iya isar da su da kyakkyawar dabi’a, sabida kyakkyawar dabi’a ta Manzon Allah (SAW), sai ya zama Uba ga sahabbansa, su kuma su kazama ‘ya’ya a wurinsa (SAW). A irin wannan halin ne agolansa dan Sayyada Khadijah, ibn Halata ya siffanta Annabi (SAW) da cewa, Annabi (SAW) ya kasance madawwamin Bushara (a ko da yaushe cikin Bushara yake yi wa al’ummarsa), madawwamin sakin fuska ne, mai taushin halayya ko saukin dabi’u, mai taushin sasanni, ba mai tsanantawa ba ne, ba mai hayaniya ba ne, ba mai fadar alfasha ba ne, ba mai aibanta jama’a ba ne, ba mai yabon jama’a ba ne na yaudara, yana kauda kai ga abin da ba ya so – sai ya nuna kamar bai san an aikata abin ba, ba a yanke kauna a gare shi – Babu wani wanda zai ce ya yi wa Annabi (SAW) wani laifi da ba zai yafe masa ba, kowa ya san wata rana in ya ba da hakuri za a yafe masa.
Ubangiji ya fada a kur’ani cewa “Fabima rahmatin minallahi linta lahum, walau kunta fazzan galizal kalbi lan faddu min haulik, fa’afu anhum wastafirlahum wa shawirhum fil amr, fa’iza azamta fatawakkal alallah, innallaha yuhibbul mutawakkilin” Da sababin rahamar Ubangiji ne kai sauki a gare su (kai Rahama ne a gare su), da ka zama mai tsanantawa, mai kaushin zuciya, da duk sai su tarwatse daga wurinka, ka nema musu afuwa ka nema musu gafara ka nemi shawararsu in za ka fara wani al’amari sannan in za ka fara ka dogara da Allah, lallai Ubangiji yana son masu dogaro a gare shi.
Ubangiji ya kara da cewa “Wala tastawil hasanatu walas sayyi’ah, idfa’a billati hiya ahsan, fa’izallazi bainaka wa bainahu adawatun ka’annahu waliyyun halim” ko kusa, Kyakkyawa ba ta yi kama da Mummuna ba, haka Mummuna ba ta yi kama da Kyakkyawa ba, ka dinga tunkude mummuna da kyakkyawa, sai ya zama tsakaninka da wanda ke kiyayya a gare ka, kai ka ce masoyinka ne (makiyinka na gaske, sai ya zama masoyinka wanda zai iya ba da jininsa a kanka).
Manzon Allah (SAW) ya kasance yana amsa kiran wanda ya gayyace shi, yana karbar kyauta in an yi masa ko da kuwa kalfatar Akuya ce aka ba shi, yana karba kuma yana sa-ka-wa a kanta.
Anas (RA) ya ce, na hidimta wa Annabi (SAW) na tsawon shekara 10 amma bai taba ce min ‘kash’ ba ko don me ya sa ka aikata kaza ko me ya sa ka bar kaza ba da dai!
An karba daga Sayyada A’isha ta ce “Babu wani Mutum daya mafi kyawun dabi’a da ya fi Annabi (SAW), babu wani daga cikin Sahabbansa ko iyalan gidansa da zai gayyaci Annabi (SAW) wani taro face ya amsa masa.
Walid dan Abdullahi yana cewa, manzon Allah (SAW) bai taba sa mun labule tsakanina da shi ba, tun daga ranar da na musulunta, bai taba ganina ba face sai ya yi min murmushi. Annabi (SAW) ya kasance yana wasan kakaci da sahabbansa yana wasa kuma da ‘ya’yansu, yana zuwa gaishe da mara lafiya da ke karshen garin Madina, yana karbar uzurin masu kafa uzuri, ba ya dauke kansa ga wanda ya zo wurin kunnensa don yi masa maganar sirri, ba ya kwace hannunsa ga wanda ya yi caffa da hannunsa har sai dai wanda ya yi caffa da hannun ya zama shi ne farkon wanda zai saki hannun.
Manzon Allah (SAW) shi yake fara yin Sallama ga wadanda ya hadu da su a yayin tafiya. Ba a taba ganin Annabi (SAW) da dai ba ya mike kafafuwansa a gaban Sahabbansa, yana girmama duk wanda ya zo masa, wani sa’in har mayafin da ke jikinsa yake cirewa ya shimfida ma bakinsa, yana yi wa sahabbansa alkunya (ba ya kiran sunayensu), ba ya yanke wa mutane magana in suna zance, sai in yaga mutumin zai shiga wata magana daban wacce ba a kanta ake kai ba.
Annabi (SAW) bai taba kabbara Sallah ba, wani ya zo yana jiransa face ya takaita sallarsa sannan ya tambaye shi bukatarsa. Annabi (SAW) ya fi duk sauran mutane kyawun murmushi kuma mafi tsarkin Rai a cikinsu.
An karbo daga Anas (RA) yana cewa, “Yaran mutan Madina suna zuwa wurin Annabi (SAW) bayan Sallar Asubah, sannan Bayi mata su zo da ruwa a cikin Akushi a kansu zuwa ga Annabi (SAW), sai ya wanke hannunshi a cikin akushin, wannan ruwan da shi za su yi karin kumallo don neman albarka. Alhamdulillah
Wasu Kadan Daga Cikin Tausayi Da Jinkai Da Rahama Ta Sayyadina Rasulallah
A halin yanzu kuma a karatun namu, za mu juya zuwa ambaton wasu kadan daga cikin Tausayi da Jinkai da Rahamar Sayyadina Rasulullah (SAW).
Tausayi da Jinkai da Rahama ta dukkanin halitta, Annabi (SAW) shi ne kan gaba. Allah Ubangiji tabaraka wata’ala ya fada cikin hakkin Annabinsa (SAW) “…Azizun alaihi ma’anittum, harisun alaikum bil mu’uminina Ra’ufun Rahim” mai girma ne a gare shi duk abin da ya wahalar da jama’arsa – ya fi damuwa da jarrabawar da ta dami al’ummarsa, mai kwadayi ne a bisa shiriyarku, dangane da Mu’uminai kuwa, Mai jinkai ne da tausayi.
Ubangiji ya kara fada kuma “Wa maa arsalnaka illa rahmatan lil’alamin” ba a turoka ba Ya Rasulallahi sai don tausayi ga halitta baki daya. (Manzon Allah (SAW) mai tausa yi ne ga halitta baki daya, ba wai sai musulmi kadai ba), ana cewa, Allah yana da Rahama 100, amma duk wannan jinkan da yake yi, daya daga cikin 100 kacal ya saukar, da mutum ya san da sauran 99 da bai yanke tsammani ga rahamar Allah ba.
Wasu daga cikin Malamai suka ce, yana daga cikin fifikon manzon Allah (SAW) cewa, Allah tabaraka wa ta’ala ya ba shi sunaye guda biyu daga cikin sunayensa (Allah): Ra’ufun da Rahimun ga Muminai. Za mu zo inda Mai littafin Ashafa, Alkadi Iyad ya tattaro sunayen Allah 30 wanda ya bai wa Annabinsa (SAW), wasu malamai kuma sun tattaro 70 daga cikin sunayen Allah wanda ya bai wa Annabinsa (SAW), wasu ma sun ce duka Asma’ullahil husna za a iya ambatar Annabi (SAW) da su sai dai ismul martabati ne kadai (Allah) ba za a kira Annabi (SAW) da shi ba.
Ibn Shihabiz zuhri (RA) ya ba da labarin cewa, wata rana Annabi (SAW) ya yi Yaki (wata kila yakin Hunaini ne) sai manzon Allah (SAW) ya ba wa Safyan dan Umayyata dan kalf tumaki 100 sau Uku. An ruwaito cewa, Sufyan ya ce, Annabi (SAW) ya ba ni abin da ya ba ni, amma kafin nan, shi ne wanda na fi kiyayya da shi a cikin mutane, amma bai gushe ba yana ba ni kyauta har sai da ya zama mafi soyuwar halitta a wurina, zan iya kashe kowa a kansa har raina ma fansa ce a gare shi.
An ruwaito cewa, wani Balaraben kauye ya zo wurin Annabi (SAW) yana neman wani abu, sai Annabi (SAW) ya ba shi abin da ya samu a wannan lokaci, sannan Annabi (SAW) ya yi masa wasan kakaci da cewa “Na Kyautata maka ya kai Balaraben kauye?”, sai ya ce, “Ina sam baka kyautata min”, sai Sahabbai ransu ya baci suka yi fushi, suka tashi suna nufin farmasa, sai Annabi (SAW) ya yi ishara gare su, su kyale shi, sai Annabi (SAW) ya tashi ya shiga cikin gida ya kara nemo wani abu ya ba shi sannan ya sake tambayarshi “Na Kyautata maka ya kai Balaraben kauye?”, sai ya ce “Na’am lallai ka kyautata min yanzun, Allah ya saka maka ya dan’uwana da alkhairi”. Sai Annabi (SAW) ya ce masa, “ka fada wani abu wanda ya bata wa Sahabbaina rai, ina so ka sake fadar addu’ar da ka yi min a gabansu, sabida abinda ke cikin zuciyoyinsu a gare ka ya fita”. Sai ya ce, zan fada musu.
Cikin yardar Allah, za mu ci gaba a mako mai zuwa.