Masu karatu assalamu alaikum wa rahmtullahi ta’ala wa barkatuh. A darussanmu na baya, mun yi bayani kan abubuwan da aka hadu kan son yawaita su da wadanda ake kin yawaita su har muka dangana da zuhudu da tsarin adon Manzon Allah (SAW).
Yanzun kuma, za mu karkata zuwa kan kyawawan dabi’un Annabi Muhammadu (SAW).
Akwai dabi’u Wahabiyya: su ne wadanda Allah ya halicci mutum da su, ana cewa tun yana yaro haka halinsa yake. Akwai wadanda kuma mutum koya ya yi.
- Rayuwar Annabi Muhammadu (SAW) Da Abin Da Ya Ta’allaka Da Aurensa (1)
- Darasi Na Biyu A Kan Matan Annabi (SAW)
Dabi’u wadanda ake tsururunsu, Malamai da masu hankali duk sun tafi cewa, dabi’u ne abin yabo ga mai ita ko da daya ce tak. Misali, wane mai hakuri ne ko mai kyauta ne da dai sauran su ballantana a ce ya tara daga cikin dabi’un da yawa ko da biyu ko uku ko fiye da haka. Dabi’u kyawawa 300 ne, Annabi (SAW) yana cewa, Allah Tabaraka wa ta’ala yana da dabi’u kyawawa guda 300 duk wanda ya siffantu da daya daga ciki zai shiga Aljannah.
Wadannan dabi’u, Shari’a ta yi yabo kuma ta yi alkawarin Aljannah ga ma’abocin daya daga cikinsu ballantana ka hada da yawa, su ne wadanda ake kira da kyawawan dabi’u “Husnul khuluki” dabi’u kyawawa suna daga cikin sashin Annabta, su ne daidaito cikin karfin zuciya da siffofinta, idan sadaukantaka Allah ya ba ka a zuciya sai a hada ta da hakuri – sadaukantaka babu hakuri zalunci kenan, in dukiya Allah ya wadata ka da ita, sai ya hada ta da kyauta, in shugabanci Allah ya ba ka sai ya hada ka da tausayi, in Malumta Allah ya ba ka, sai ya hadaka da soyayyar shiriyar mutane. Duk irin dabi’ar da Allah ya ba ka, sai ya hada ta da tsaka-tsaki.
Shari’a ba ta son ka zama keke-da-keke, ma’ana kar ka yi sama kololuwa ba ka tsoron kowa kuma kar ka yi kasa can ka zama raggo, Shari’a tana son daidaito.
To mu sani cewa, duk wannan kyawawan dabi’un su ne dabi’un Annabinmu (SAW). Duk abubuwan da Allah ya bai wa Annabi (SAW) don mu san dabi’u su ne gaba, sai Allah ya yi kirari yana yabon Annabi (SAW) da cewa, Ya Rasulallahi, wallahi kana kan dabi’u masu girma da fadinsa cewa “Wa’innaka la’ala khulukin azim”. Sayyada A’isha tana cewa, dabi’un Annabi (SAW) su ne ‘Alkur’ani’ yana yarda da abin da alkur’ani ya yarda da shi, yana fushi da fushin Alkur’ani. “…kana khulukuhul kur’anu, yarda bi ridahu, wa yaskhadu bi sakhadihi”, Annabi (SAW) ya ce, Allah ya aiko ni don in cika kyawawan dabi’u “Bu’istu li’utimmima makarimal akhlaki” tun daga kan Annabi Adam (AS), akwai dabi’u kyawawa akwai na banza har aka zo kan Kuraishawa, don haka Annabi (SAW) ya ce, yanzun an aiko shi don cika kyawawan dabi’un kuma ya cika su, don haka yanzun, kowa sai ya yi koyi da na Annabi (SAW).
Anas Allah ya yarda dashi ya ce, Annabi (SAW) ya kasance mafificin mutane a kan kyawawan dabi’a, “kana Rasulallahi (SAW) ahsanan nasa khulukan” ba laifi ba ne a fi ka karatu da arziki amma kar ka bari a fi ka dabi’a.
An karvo daga Sayyadina Aliyu bin Abi Dalib, akan irin Hadisin da ya gabata daga Anas. Wani ya tambayi Sayyadina Ali a kan ya lissafa masa dabi’un Annabi (SAW), sai Sayyadina Ali ya ce masa kafin na fada maka, zan so ka fara lissafa min kayayyakin jin dadi da Allah ya ambata, sai ya ce suna da yawa ba za su lissafu ba, sai Sayyadina Ali ya ce, amma kuma Allah ya ce musu ‘yan kadan “Mata’ud duniya kalil…” ta yaya zan lissafa maka abin da Allah ya ce masa mai girma “Wa’innaka la’ala khulukin azim”.
Yana daga abin da Malamai muhakkikai (karshen yabon da za a yi wa Malami, a ce masa muhakkiki, wasu mutane ne daban suka vata wannan suna amma asalinta yana nan) suka tabbatar cewa, wadannan kyawawan dabi’u a kansu aka halicci Annabi (SAW). Mala’ikah Ridwan mai tsaron Aljannah, Allah ya dunkule ni’imarsa ce ya halicce shi da ita, Mala’ikah Maliku mai tsaron wuta, fushin Allah, Allah ya tattare ya haliice shi da ita. Don haka babu abin da zai zo ta wurin Ridwan sai ni’ima kamar yadda Malik babu komai sai fushi.
Annabi (SAW) babu abin da zai zo ta wurin shi sai Ni’imah, wani zai iya cewa ai ya yi yaki, yaki kuma azaba ce, sai mu ce masa wannan magani ne Annabi (SAW) ya ba da kamar irin yadda Uba yake bai wa Dansa magani madaci don yaron ya warke daga cuta ba don azabtarwa ba, kamar yadda Malamin makaranta ke dukan Dalibansa ba don azabtarwa ba sai don ladabtarwa.
Wanda ya samu tarihin Annabawa tun daga kuruciya har zuwa lokacin aiken Annabta, zai tabbatar da kyawawan dabi’un Annabawa, sabida ba koya suke yi ba, da ita ake halittarsu. Annabi (SAW) ya ce, Ubangijina ne ya ladabtar da ni kuma ya kyautata ladabtarwata “Addabani Rabbi fa ahsana ta’adibi” an ga irin wannan ladabtarwar a wurin Annabi Isah da Musa da Sulaiman da Yahya (Alaihimus salam) da sauransu.
Haka Allah ya halicce su da wadannan kyawawan dabi’un da Ilimin Hadarar Allah.
Amma wadanda ba su da wannan dole sai sun koya sun hadu da Malaman da suka sani, sannan su sanar da su kamar yadda aka sanar da su, in mai neman Allah ne ya samu Shehi ya ba shi azkaru tarbiyyati da dai dukkan fannin dabi’u.
Allah yana cewa cikin hakkin Annabi Yahya (AS) “wa atainahul hukma sabiyya” Malamai masu tafsiri suka ce, Allah ya bai wa Annabi Yahya Ilimin Injila, ya haddace, ya san lunguna da sako na ma’anoninta tun yana yaro. Malam Ma’amaru ya kara da cewa, tun yana dan shekara biyu ko uku ya san duk wadannan ma’anonin littafin. An ruwaito cewa, wata rana yara sun tambaye shi, wai me ya sa baka wasa? Sai ya ce musu, ba sabida wasa aka halicce ni ba.
Mahaifinsa Annabi Zakariya yana da kusan shekara 120, mahaifiyarsa tana da kusan shekara 80 Allah ya azurta su da samun Yaro (Annabi Yahya). A al’adar Mahaifi yana son wasa da dansa a lokacin kuruciya amma Annabi Yahya duk lokacin da a kai masa wasa, sai ya nuna rashin jin dadin wasan, har wata rana yake ce wa Mahaifinsa Annabi Zakariya (AS), wai kai wasa kazo yi Duniya ne? Hakan ta sa Annabi Zakariya ya koma kai kukansa ga Ubangiji kan halayen Dansa, Annabi Yahya. Sai Ubangiji ya ce masa, Ya Zakariya, kai ka roke ni in ba ka shi a haka a wurin addu’arka “Rabbi habli min ladunka waliyyya, yarisuni wa yarisu min ali ya’akub, waj’alhu rabbi radiyya” ka nema Ubangijinka ya ba ka Da waliyyi daga wurinsa kuma ya gaje ka da duk wani gadon gidan Annabi Ya’akub (Annabawa 124,000 duk ba ni Isra’ila ne sai ‘yan kadan) kuma Ubangiji ya sanya shi yardajje. Me irin wannan abubuwan ba zai iya tsayawa wasa ba.
An ruwaito cewa, Uba ya yi wasa da dansa a shekaru bakwai na haihuwa, ya karantar da shi a shekaru bakwai na biyu na haihuwa, ya zama abokin dansa a shekaru bakwai na Uku na haihuwa daga nan ya bar shi da makarantar Duniya.
Allah Ubangiji tabaraka wa ta’ala ya bayyana kalaman Annabi Isah (AS) ga mahaifiyarsa yayin haihuwa: “fa nadaha man tahtiha alla tahzani kad ja’ala rabbuki tahtaki sariyya” Sai wanda ke karkashinta, ya kirata da cewa, kar ki yi bakin ciki, lallai Ubangijinki ya sanya abin da ke kasanki ya zama farin ciki a gare ki.