A watan Nuwambar shekarar 2021 ne aka gudanar da taro karo na 8, na ministocin kasashe mambobin dandalin bunkasa hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka ko FOCAC, ta kafar bidiyo daga Dakar na kasar Senegal.Â
Yayin taron, an amince da wasu manufofi, ciki har da yarjejeniyar Dakar. A kuma lokacin ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da kaddamar da wasu shirye shirye guda 9, na raya hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka.
Masharhanta na kallon wannan shirye shirye a matsayin ginshikai da zai kara karfafa kawancen gargajiya tsakanin Sin da Afirka, za su kuma ingiza burin da ake da shi, na gina al’ummar Sin da Afirka mai kyakkyawar makomar bai daya a sabon zamani da muke ciki.
Yanzu haka, an shafe shekara daya ko fiye tun bayan gudanar da wancan taro na ministoci. Kuma duk da cewa an samu manyan sauye-sauye a harkokin kasa da kasa, da tarin kalubale, da yanayi na rashin tabbas a wasu sassa, a daya bangaren Sin da kasashen Afirka, sun ci gaba da aiwatar da matakan goyawa juna baya, da zurfafa kyakkaywar alakar su yadda ya kamata. Kaza lika sassan biyu sun cimma nasarori masu yawa a fannin cin gajiyar juna.
Sin da Afirka, sun ci gaba da raya dangantakar su, da wanzar da adalci a harkokin da suka shafi kasa da kasa, sun kuma rungumi ci gaban su cikin hadin gwiwa, suna yaki da kamfar abinci, yayin da Sin ke taimakawa kasashen yankin kahon Afirka dake fama da fari da abinci gwargwadon karfin ta, kana sassan 2 suna aiki tare wajen yaki da annobar COVID-19, da sauran matsalolin lafiya da sai sauran su. Alal misali, kasar Sin ta taimakawa AU wajen gina wata cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Afirka.
Ko da a baya bayan nan ma, wata tawagar jamian lafiya ta Sin, ta tashi daga birnin Shijiazhuang, fadar mulkin lardin Hebei na arewacin kasar Sin, zuwa janhuriyar dimokaradiyyar Congo. Tawagar da aka tsara za ta yi aikin tallafawa harkokin kiwon lafiya a kasar na tsawon shekara daya.
A bana ake ciki shekaru 50, tun bayan da lardin Hebei na kasar Sin, ya fara tura jamian lafiya masu aikin jin kai zuwa kasashen waje. Kuma tun fara gudanar da wannan muhimmin aiki ya zuwa yanzu, lardin na Hebei ya tura rukunonin jamian lafiya 21 zuwa janhuriyar dimokaradiyyar Congo.
Wannan dai bangare daya ne kawai, cikin muhimman fannoni da Sin ke samarwa kasashen Afirka taimako, karkashin alkawuran da Sin din ke yiwa ’yan uwan ta kasashe masu tasowa musamman ma kasashen Afirka. Don haka a iya cewa, kasar Sin na cika alkawura da take dauka ga kasashen Afirka yadda ya kamata. (Saminu Hassan)