Layusa ta zo ta shaida masa sakon da aka aiko ta, ya yi murmushi ya ce; “Ki gaya mata ina amsawa, sannan ki sanar mata ni ma ina karanta mata gaisuwa, kuma ina sauraronta nan da rabin sa’a, in kuma dokina ya yi kuka sau uku ba ta fito ba, to za ta fito ta samu ba na nan, saboda ina da abin da ya fi ta muhimmanci a gabana.”
Layusa ta ce; “Amma kuma ta yi min umarni in kai ka inda za ka zauna ka dan huta kafin ta fito.” Shahid ya sauko ya shiga ya zauna.
- Ma’aikatan Gwamnati Sun Fi ‘Yan Siyasa Cin Hanci Da Rashawa – Kwamitin Majalisar Dattawa
- 2023: INEC Ta Yi Wa Jam’iyyu Karin Haske Kan Dokar Kamfen Da Tarukan Siyasa
Da zuwan Layusa ta same ta tana kokarin shiga wanka, kuma ta san ta kan jima kafin ta fito, a nan ta fada mata sakonsa.
Ko da jin an ce idan doki ya yi kuka sau uku zai tafi, sai ta waigo a fusace ta ce; “Meye kuma na alakanta doki da zuwana, Shahida kin ji irin abin da nake magana a kai ko?
Ke koma ki fada masa ya sake tunani, kuma ya sani da mutum zai yi magana ba da dabba ba, saboda me zai yi kokarin hada wannan lamarin da dabba, ko ya manta doki dabba ne? Maza je ki sanar masa cewa, ya sauya tunaninsa don mu ba dabbobi bane.”
Gama kalamanta ke da wuya, suka jiyo haniniyar doki ta farko, Layusa ta yi sauri ta tafi don ta sanar da shi.
Da isarta wurinsa sai doki ya sake yin wata haniniya karo na biyu, sai ta yi kicibis da shi ya tafi wurin dokin, a nan ta sanar da shi sakon da aka umarce ta, ta fada masa.
Shahid ya yi murmushi yana shafa dokinsa, ta waiga don ta koma cikin gida, sai ta hango su Hafida tafe a tsakiyar fulawowi, ta yi ajiyar zuciya.
Da zuwansu suka shiga dakin da aka sauke shi suka zauna, ya juyo ya taho, Layusa na gaba yana biye da ita.
A nan yake riyawa a ransa cewa, wadda tafi kowacce kwalliya a cikinsu ita ce Hafida, saboda ita ce ta yi kwalliya yanzu, sannan kuma ita ce mai masaukin baki.