Wani malami a Jihar Borno, mai suna Hassan Bukar, ya koka kan yadda ya shafe watanni 20 yana aiki ba tare da albashi ba saboda zargin rashin halartar aiki na mako uku. Bukar, malamin Turanci a Makarantar Sakandare ta GSS Damasak, ya bayyana cewa bai halarci aiki ba ne saboda yana kula da matarsa da ke jinya a asibiti.
Duk da cewa ya rubuta wasiƙun neman afuwa kuma ya koma bakin aiki, har yanzu ba a mayar masa da albashinsa ba. Ya ce shugaban makarantar, Alhaji Shettima Ali, ya wanke shi daga zargin guduwa daga aiki kuma ya yaba da ƙoƙarinsa, amma har yanzu gwamnati ba ta mayar masa da albashinsa ba.
- Ƴan Ta’adda Sun Sako Manoma 11, Sun Rike 3 A Borno
- Ƴan Ta’adda Sun Sako Manoma 11, Sun Rike 3 A Borno
WikkiTimes ta ruwaito cewa, Bukar ya ce ya sanar da Kwamishinan Ilimi na Jihar Borno game da matsalarsa yayin da ya ziyarci makarantar, inda aka yi alƙawarin shawo kan matsalar. Sai dai duk da an gayyace shi zuwa ofishin kwamishinan, an hana shi shiga sau da dama.
Saboda ƙuncin rayuwa da dogon shiru daga ɓangaren hukumomi, ya yanke shawarar amfani da kafafen sada zumunta don riƙon a cire masa takunkumin albashinsa. Ya bayyana cewa yana da iyali da ya ke kula da su, kuma matsin tattalin arziƙi ya ƙara dagula lamarinsa.
A martaninta, hukumar kula da Malaman Jihar Borno (TSB) ta musanta zargin dakatar da albashin malamai saboda rashin halartar aiki na mako uku kacal. Jami’ar hulɗa da jama’a ta hukumar, Zara Aji Monguno, ta bayyana cewa kawai malamai da suka daɗe ba tare da sun halarci aiki ba, kamar tsawon zangon karatu, aka dakatar da albashinsu. Ta kuma ce sabon shugaban hukumar ya fara ɗaukar matakan mayar da albashin malamai da abin ya shafa, kuma wasu sun riga sun fara karɓar haƙƙoƙinsu. Duk da haka, ta jaddada cewa dole ne a bi ƙa’idojin neman izinin rashin zuwa aiki.
Sai dai Bukar ya musanta wannan iƙirari, yana mai cewa ya sanar da shugabansa kuma ya bi duk matakan da suka dace, amma har yanzu ba a bi masa haƙƙinsa ba. Ya ce sau da dama an buƙaci ya kawo bayanan asusun ajiyarsa na banki don duba matsalarsa, amma babu wani canji. Duk da cewa shugaban makarantar ya wanke shi daga zargin guduwa daga aiki, har yanzu ba a mayar masa da albashinsa ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp