A ranar 15 ga watan Mayun 2015, tsohon shugaban kasa Godluck Jonathan ya rattaba hannu kan dokar dakile aikata laifuka ta internet, inda ya zama doka.
Manufar sanya dokar ita ce domin dakile matsalolin aikata laifuka ta intanet, damfarar kwamfuta da kuma ta’addanci ta yanar gizo.
- Yadda Wike Ya Kafa Tirihin Gudanar Da Ayyukan Ci Gaba A Abuja
- Rashin Wadatar Kayan Aiki: Yadda Nijeriya Ta Kasa Dakatar Da Asarar Naira Tiriliyan 1.4 A Sashen Kiwon Lafiya
Dokar kai tsaye an yi ta ne domin dakile yawan damfara, musamman ma a kafafen sadarwar zamani ko inda wasu kwararru ke kira sabbin hanyoyin sadarwa.
Dokar, ita ce ta farko a Nijeriya da ta bayar da dama ga hukumomi su bincika, dakilewa, magancewa, haramtawa, da kuma gurfanar da laifukan internet a Nijeriya.
Daya daga cikin laifukan da suka sa aka sa hannu kan dokar har da wani mummunan kisan da aka yi wa wata dalibar jami’ar Jihar Nasarawa, Cynthia Osokogu a shekarar 2012, inda wasu makasanta suka mata tarko daga Legas zuwa Abuja tun a dandamalin sada zumunta na Facebook.
Sun mata fashi tare da yi mata fyade har suka kasheta a otel. Daga bisa dan ta’addan da ya jagoranci hakan ya fuskanci hukuncin kisa ta hanyar rataya daga babbar kotun Jihar Legas.
Tun daga wancan lokacin a cewa masu ruwa da tsaki wajen aikata laifuka da boyewa ta yanar gizo suna tafka ta’asa na karuwa a Nijeriya.
Dokar wadda aka yi mata kwaskwarima ya biyo bayan da wasu masu ruwa da tsaki da kungiyoyi suka nemi ka da a tauye hakkin fadin albarkacin baki da
hakkin ‘yan jarida, dokar wacce Shugaban kasa Bola Tinubu ya sa wa hannu ta zama doka a ranar 28 ga watan Fabrairun 2024.
Yayin da duniya ke kara rungumar amfani da yanar gizo, barazanar aikata laifukan yanar gizo na kara karuwa, inda hukumomi da masana shari’a ke ci gaba da yin nasu kokarin wajen ganin an samu sauki.
Ganin yadda ake yawan samun aikata laifuka ma ya sanya masu ruwa da tsaki suna ganin akwai bukatar sake nazartar dokokin da aiwatar da tsare-tsaren da suke nan domin tabbatar da kare wadanda tsautsayin laifukan yanar gizo ya shafa.
Cin zarafi ta yanar gizo ya zama ruwan dare a Nijeriya, inda wasu ke amfani da wannan damar ko fasahohi wajen cin zarafi, barazana da bata sunan wasu a yanar gizo.
Cin zarafin da suke faruwa a emails, sakon karta kwana, wallafe-wallafe a kafafen sadarwar zamani na zama babban abin damuwa idan ya kasance da bata kima da suna da cin mutunci ko sharri ko kage.
Irin wadannan cin zarafin kai tsaye na zuwa kan wadanda aka nema ci wa zarafi a wasu lokutan ma har tana da zaune tsaye laifukan yanar gizo ke haifarwa, a yayin da wani lokacin kuma wadanda tsautsayin ya shafa ya kan shiga damuwa da firgici ko sa shi jin kunyar jama’a.
Wasu lokutan masu tafka ta’asar kan yi sharhi ko fuskantar duk wani abin da ya shafi wanda suke hara kai tsaye, yayin da suka wallafa wani abu a yanar gizo.
A wasu lokutan kuma masu aikata irin wannan laifin kan bude shafukan bogi domin tafka ta’asarsu, da aike wa da sakonni domin ka da a yi saurin gano su ko kama su, a yayin da a gefe guda kuma suke bata wanda suka sa a gaba.
A cewar babban jami’in gudanarwa na cibiyar kula da lafiya ta GreyHub, Dakta Olusola Olowookere, ya ce, laifukan yanar gizo sun hada har da yin amfani da kafafen sadarwa wajen cin zarafin wani ko wasu, haifar da fargaba da tsoro ko tozarci.
Olowookere ya shaida wa LEADERSHIP cewa a wani bincike da hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta gudanar ta gano kashi 37 na masu amfani da yanar gizo sun taba fuskantar nau’o’in cin zarafin yanar gizo ko laifukan da suka shafi intanet.
“A cewar wani bincike da cibiyar Cyber ‘Awareness and Debelopment’, a kalla kaso 20 na matasan Nijeriya sun taba fuskantar cin zarafin yanar gizo,” ya shaida.
A baya-bayan nan ‘yan Nijeriya da dama ne aka samu da laifukan ta’addanci a intanet, inda aka kama su da laifukan bata suna ko cin zarafi.
A ranar 2 ga watan Agusnatan 2023, mai shari’a Nicholas Oweibo ya daure wata mata mai suna Okoye Blessing Nwakaego shekaru uku a gidan yari kan cin zarafin wata tauraruwar masana’ar fina-finai ta kudancin Eniola Badmus.
Nwakaego an kamata da yin amfani da wayarta ta hannu wajen wallafa cin zarafi, tozarci, karya da kage a kan tauraruwar a shafin Tiktok da wasu kafafen sadarwar zamani na yanar gizo.
Sannan, a ranar 7 ga watan Nuwamban 2023, mai shari’a Nathaniel Ayo-Emmanuel na babbar kotun tarayya da ke Osogbo a Jihar Osun, ya daure wasu mutum shida kan kama su da laifin cin zarafi ta yanar gizo, yin sata da damfarar tsohon shugaban majalisar dokokin Jihar Osun, Timothy Owoeye, har naira miliyan 38.
Wadanda aka dauresu su ne Kazeem Agbabiaka, Rasheed Ojonla, Babatunde Oluajo, Adebiyi Kehinde, Femi Oseni da Oyebanji Oyeniyi, inda aka gurfanar da su a gaban kotun a ranar 19 ga watan Oktoban 2018, kan zargin laifuka hudu da suka hada da ta’addanci, damfara, cin zarafi a yanar gizo.
A hukuncinsa, mai shari’a Ayo-Emmanuel ya ce wadanda aka yanke wa hukuncin sun aikata laifukan ne da suka janyo kunci ga wanda suka yi don haka ba su cancanci wani sassauci ba.
Ko da yake, an zargi ‘yansanda da yin amfani da sashin dokar yanar gizo na 24 wajen cin zarafi da tozarta ‘yan jarida. Alal misali, a ranar 22 a watan Agustan 2019, wani dan jarida mai suna Agba Jalingo, ‘yansandan Jihar Legas sun cafke shi kan zarge-zargen aikata laifukan cin zarafi ta yanar gizo.