Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana cewa, lalacewar babban hanyar raba wutar lantarki ya kara bayyana gazawar gwamnatin tarayya a zahirance ne.
LEADERSHIP ta rawaito cewa a sakamakon lalacewar na’urar raba wutar lantarkin an fuskaci duhu a fadin Nijeriya tun daga karfe 6.49 na ranar Lahadi har zuwa safiyar ranar Litinin.
- Tinubu Bai Wuce Nauyin Dan Jariri Ba Idan Aka Kwatanta Shi Da Atiku —Dino Melaye
- Zabar Mataimaki: Akwai Alamun PDP Ka Iya Zabar Muo Aroh Matsayin Mataimakin Atiku
Atiku ya wallafa a shafinsa na yanar gizo a yammacin ranar Litinin cewa, muddin ‘yan Nijeriya na neman mafita, to ko da wasa kada su kada su zabi jam’iyyar APC domin kuwa matsalolin da ta kasa shawo na da yawa.
Atiku ya kara da cewa, wannan matsalar duhu da aka shiga kari ne kan matsalolin da suka hada da na tsaro da tattalin arziki da rugujewar ilimi da zubar da kima da mutuncin dan Adam karkashin mulkin APC.
“Fatana shi ne ‘yan Nijeriya za su yi gaggawar yin rugu-rugu da APC ta hanyar amfani da katin kuri’unsu domin gina sabuwar Nijeriya domin cika burin mafarkinmu na sake farfado da Nijeriya.”