• English
  • Business News
Saturday, November 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Lalacewar Tarbiyar Dalibai Mata A Makarantun Islamiyya Da Na Boko

by Rabi'at Sidi Bala
7 hours ago
Boko

Shafin TASKIRA shafi ne da ya saba zakulo muku batutuwa daban-daban, wadanda suka shafi al’umma. Ciki sun hadar da; zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya da dai sauransu.

Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da abin da ya shafi lalacewar dalibai mata a makarantun islamiyya da kuma na boko, wanda dalilin hakan ya sa muka ji ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin game da wannan batu;

  • Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 
  • Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

“Ko me yake kawo yawaitar lalacewar dalibai mata a makarantun boko da kuma Islamiyya a cikin al’umma, wanda ke wargaza tarbiyyar yara gabadaya?, Mene ne dalilin lalacewar wasu daga cikin dalibai bayan ana ganinsu da kamun kai, wasu kuma ba za a shedi halayyarsu ba?, Wacce shawara ya kamata a bawa iyaye da dalibai domin kulawa da kansu da kuma karatunsu?”.

Gadai bayanan nasu kamar haka; Sunana Princess Fatima Mazadu, Gomben Najeriya:

Abu na farko shi ne, son abun duniya da wasu yaran ke sakawa zuciyarsu, sannan wasu suna koya ne daga wajen kawayen da suke tare da su. Wasu ko da dabi’unsu masu kyau ne, watarana sukan tsinci kansu sakamakon gudun shiga matsala, idan za su samu taimako daga wajen wani sai su bar tarbiyyar da aka koya musu daga gida. Wasu kuma kaddara ce ta rayuwa, da kuma talauci, wasu kuma iyayen ne da kansu ke koya musu yadda za su lalace wajen nemo abin duniya, wasu kuma rashin kula ne da iyaye ba sa yi a kan ‘ya’yansu. Akwai abubuwa da yawa da yake janyo haoan. Ya kamata iyaye su sani su fa yara amana ce Allah ya danka musu, kuma za a tambaye su amanar da aka basu a lahira.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Shagwaɓa Kananan Yara Da Kudi Ke Shafar Tarbiyyarsu

Tsokaci A Kan Mata Masu Tsananin Kishi

Sunana Lawan Isma’il (Lisary), Rano, A Jihar Kano:

Haduwa da kawayen banza da kuma kuntatawa da wasu malaman suke nuna musu, saboda kin amincewa da su na bukatun da suke nema a wajensu. Da yawa iyayen ba sa tsayawa su saurari matsalolin ‘ya’yansu kan abin da ke damunsu a makaranta, da kuma rashin bibiyar karatunsu da abokansu. Iyaye su tabbatar da suna bawa yara kudi da kayan abincin da zai ishesu idan a makarantun kwana suke, sannan su tabbatar da tarbiyyar malaman da za su kai yaran nasu.

Sunana Aisha Isah Gama (Mai Waka), Jihar Kano:

A gaskiya abin da ke janyo wa baya wuce gurba tattun abokai, har da lefin malamai saboda malami ne za ka ga ya kulla soyayya da daliba, kin ga matsala ta farko kenan, sai mu’amala da kawaye marasa tarbiyya, za ki ga baki ragi ‘yar ki da komai ba, amma kawaye sun bata ta. Shawara iyaye mu kula da ‘ya’yanmu, mu ja su a jiki su zama abokan mu, mu rika tunawa kiwo Allah ya ba mu kuma zai tsayar damu ya yi mana tambaya akan kiwon da ya bamu, mu raba su da kawaye.

Sunana Hauwa Abubakar Sarki, daga Suleja, Jihar Neja:

Sautari malamai su ne silar lalacewar dalibai akowane makaranta, daga na islamiyar har na bokon. Ka ga malami ya rasa wacce zai yi soyayya da ita sai dalibar sa, duk da ba haramun bane, amma ba sa bin hanyar da ya dace wajan neman soyayyar daliban nasu. Malamai su ne silar lalacewar wasu daga cikin dalibai, daga lokacin da malami ya nuna kwadayi akan abin hannun dalibar sa walau surar da Allah yayi mata ko kuma abun hannuta (kudi) babu magnar tarbiyya a nan wajan. Sautari babu kyau, saboda duk inda aka ce malami to fa matsayin uba yake ga dalibansa. Su ma kuma dalibai su kasance masu kamu kai da nuna kyakkyawan tarbiyya a duk inda suke.

Sunana Hafsat Sa’eed:

Sai dai in ba tarbiyya suka samu tun farko ba,idan har sun samu tarbiyya, kuma an magance musu matsalolin da ba za su ga wani abu su yi sha’awa ba, ba na tunanin yaro zai lalace. Amma rashin hakan yaro na iya shiga cikin wani yanayi. Wasu kuma akwai tarbiyyar amma sakamakon haduwa da kawaye sai su canja, domin kawa tana iya canja kawa a lokaci daya. Amma akwai wadanda jarrabawa ce, idan Allah ya jarabce ka babu yadda za ka yi sai ka karba ka yi ta addu’a.

Sunana Muktari Sabo Jahun A Jihar Jigawa:

Na farko dai akwai matsalar Tarbiyya wadda ita ce tushen komai, sannan kuma da rashin gata ga wasu, wasu kuma neman abin duniya ne yake kai su ga lalacewa. Munanan abokai kan iya bata abokansu, haka kuma rashin bibiyar iyaye akan lamarin ‘ya’yansu har sai sun fada wani hali. Iyaye su sa hankali da lura akan yaransu, kuma su dage da yi musu addu’a, kuma su san su waye abokan ‘ya’yansu.

Sunana Fatima Nura kila, Jihar Jigawa:

Abin da yake janyo wa mafiya yawa shi ne, san zuciya, kusan shi ne kaso 70% na lalacewar dalibai mata a makarantu. Yana faruwa ne mata sun dau karya sun dorawa rayuwarsu, wata iyayenta rufin asiri gare su, za ta ce sai ta yi abin da kawarta ta yi, bayan samun iyayen kowanne daban. Shawarar ita ce, a kodayaushe mu mata mu daina kallan saman mu, a kodayaushe mu rika kallon kasan mu, hakan shi ne zai sa mana wadatar zuci.

Sunana Hassana Sulaiman, Hadejia, A Jihar Jigawa:

Daga cikin abin da ke kawo lalacewar dalibai musamman ma mata a makarantun boko da kuma islamiyya cikin al’umma, wani lokacin rashin sanin su kansu ne da iyayen basu fiya duba da lamuran yaran nasu matan ba. Dalilin lalacewar wasu daga cikin dalibai a wannan lokacin bai huce na kawaye ba. Saboda kawaye suna taka muhimmiyar rawa wani lokacin fiye ma da iyayensu. Ya kamata iyaye musamman mata, su zama kawaye ga ‘ya’yan nasu dan ta haka ne ‘ya’yan nasu matan za su iya sakin jiki da su suna zaman fira tare a hakan iyayen za su fahimci su waye ne ma yaransu, kuma wani abu ne a ransu wanda za su iya basu shawarar yadda za a magance matsalar maimakon lalacewar su ta sanadiyyar kawaye.

Sunana Hassana Yahaya Iyayi, Jihar Kano:

Yawanci soyayya da malamai ke yi da dalibai shi yake jawo wa. Kin ga kawaye sune kan gaba wajen canja wa yara dalibai tarbiyya da kuma ita soyayyar da malaman ke shinfidawa da yaran. Iyaye dai su rika kulawa da tarbiyyar ‘ya’yansu dan kuwa amana ce Allah ya dora a hannunsu.

Sunana Nabila Dikko, Argungu, Jihar Kebbi:

Lalacewar ɗalibai mata na yawaita ne saboda rashin kulawar iyaye, rinjayar abokai marasa tarbiyya da amfani da kafafen sada zumunta ba tare da iyaka ba. Wasu suna da kamun kai saboda tarbiyyar gida, wasu kuma babu. Shawara, iyaye su kula da ‘ya’yansu, dalibai kuma su tsare mutuncinsu, su mayar da hankali ga karatu.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yadda Shagwaɓa Kananan Yara Da Kudi Ke Shafar Tarbiyyarsu
Taskira

Yadda Shagwaɓa Kananan Yara Da Kudi Ke Shafar Tarbiyyarsu

October 19, 2025
Kishi
Taskira

Tsokaci A Kan Mata Masu Tsananin Kishi

October 12, 2025
Illolin Da Ke Tattare Da Mallaka Wa Kananan Yara Wayar Hannu
Taskira

Illolin Da Ke Tattare Da Mallaka Wa Kananan Yara Wayar Hannu

October 4, 2025
Next Post
Kamfanoni Masu Jarin Waje Na Samun Kwarin Gwiwa Daga CIIE

Kamfanoni Masu Jarin Waje Na Samun Kwarin Gwiwa Daga CIIE

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

November 8, 2025
Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

November 8, 2025
Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

November 8, 2025
Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

November 8, 2025
Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

November 8, 2025
Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko

Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko

November 8, 2025
CMG Ya Watsa Jerin Shirye-Shirye Don Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

CMG Ya Watsa Jerin Shirye-Shirye Don Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

November 8, 2025
CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

November 8, 2025
Xi Ya Yi Kiran Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa A Yayin Rangadin Aiki A Guangdong

Xi Ya Yi Kiran Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa A Yayin Rangadin Aiki A Guangdong

November 8, 2025
Ta’aziyyar Rasuwar Jarumin Kannywood, Malam Nata’ala

Ta’aziyyar Rasuwar Jarumin Kannywood, Malam Nata’ala

November 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.