Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC), Ola Olukoyede, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su shiga cikin aikin sa ido kan ayyukan mazabu da ‘yan majalisunsu ke aiwatarwa.
Da yake jawabi a Kano yayin taron yini ɗaya na tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan “Inganta bindiddigi, da tabbatar da gaskiya, da riƙon amanar Jama’a wajen aiwatar da aiyukan mazaɓu a Nijeriya,” wanda cibiyar nazarin Dimokuraɗiyya ta Aminu Kano ta shirya, Olukoyede ya jaddada muhimmancin al’umma su riƙa yi wa shugabanni hisabi domin bunƙasa cigaba.
- Kotu Ta Hana EFCC Kama Rabi’u Musa Kwankwaso
- Jami’an Tsaro Sun Tsinci Wata Jaririya Da Aka Jefar A Kano
Olukoyede ya bayyana muhimman matakai guda biyar don inganta gaskiya da bin diddigin ayyuka: haɗin kan al’umma, da gaskiya a cikin kuɗaɗen ayyuka, da ƙarfafa hanyoyin sa ido, da samun bayanai ga jama’a, da haɗin gwuiwa da hukumomin yaƙi da cin hanci. Ya jaddada cewa, dole ne a sanar da jama’a adadin kuɗin da aka ware don aiki, da bayanan kwangiloli, da lokacin kammala aikin domin su iya bibiyar cigaba yadda ya kamata.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su shiga cikin yaƙi da cin hanci, yana mai tunatar da su cewa yaƙi da laifukan kuɗi aiki ne na kowa. Olukoyede ya nuna cewa cin hanci yana hana cigaba kuma yana lalata aminci tsakanin jama’a da gwamnati, yana mai jaddada muhimmancin gaskiya a cikin yaƙi cin hanci.