Lauyoyin Majalisar Dattawa sun ƙaryata ikirarin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan kan cewa kotun tarayya ta umurci a dawo da ita bakin aiki daga dakatarwar da aka yi mata.
Lamarin ya biyo bayan wani faifan bidiyo ya yaɗu a kafafen sada zumunta, inda Sanatar ta Kogi ta ce za ta koma bakin aiki bisa hukuncin da Mai Shari’a Binta Nyako ta yanke a ranar 4 ga Yuli.
- Ranar Talata Mai Zuwa Zan Koma Zauren Majalisar Dattawa – Sanata Natasha
- Kotu Ta Umarci Majalisar Dattijan Nijeriya Da Ta Gaggauta Janye Dakatarwar Da Ta Yi Wa Natasha
Lauyoyin Majalisar, ƙarƙashin jagorancin Paul Daudu & Co., sun bayyana cewa kotun ba ta bayar da wani umarni kai tsaye da ke soke dakatarwar watanni shida da aka yi mata ba. Sun kuma jaddada cewa hukuncin bai ƙunshi wata doka kai-tsaye da ke tilasta wa Majalisar ta dawo da ita ba, saɓanin yadda Sanata Akpoti-Uduaghan ta fassara.
Lauyoyin sun ƙara da cewa alkaliyar kotun kawai ta bayyana ra’ayi ne kan cewa dakatarwar na iya yin yawa saboda ‘yancin wakilcin jama’a, amma ba a mayar da ita ba.
Lauyoyin Majalisar sun gargaɗi jama’a da ka da su rikita hukuncin kotu, domin hakan na iya kawo ruɗani da shafar alaƙar da ke tsakanin ɓangarorin gwamnati. Sun kuma ce har yanzu ba a fitar da cikakken kwafin hukuncin ba, don haka kowa ya jira kafin ɗaukar mataki.
A ƙarshe, lauyoyin Majalisar sun ja hankalin lauyoyin Sanata Akpoti-Uduaghan da su yi taka-tsantsan don kauce wa yi wa kundin tsarin mulki kutse ko sanya rikici a majalisa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp