Abubuwa masu dadi na faruwa a dakin kwana, wuri ne na hutawa da kuma sabunta kwanji. A can ne wani lokaci a shekarar 2004, Sam Nda-Isaiah da uwargidansa Zainab suka yi tunanin kafa gidan jarida.
Ta bayar da labarin yadda aka wayi gari kwatsam maigidanta ya tashi ya dauki biro da takarda ya fara ‘yan rubuce-rubuce, daga nan ya tambaye ta ko ya take ganin sunayen da ya rubuta da kuma tsarin zanen da ya yi. Tabbas ba a wannan ranar ce aka fara jaridar ba. Amma lokaci kawai ake jira ya yi.
- Kasar Sin Ta Kakaba Takunkumai Kan Wasu Kamfanonin Amurka 3 Da Manyan Jami’ansu 10 Don Gane Da Batun Sayarwa Yankin Taiwan Makamai
- Majalisa Ta Amince Jami’an Kiyaye Haɗurra Su Riƙe Bindiga
Wannan hikima wadda daga bisani ta zama Jaridar LEADERSHIP, ta samo asali ce bayan wani abu mai sosa rai ya faru shekaru 20 da suka gabata; inda ta zama kamfanin jaridu da ke kunshe da jaridu marasa tsoro da ke da karfin fada a ji. Don haka, bari mu yi waiwaye a cikin shekarun nan da aka samu wannan ci gaba
Dakin gwajin harhada magunguna
Sam, kamar yadda ake kiran wanda ya kafa; dan jarida ne mai harhada magunguna (Pharmacist). Mahaifinsa Clement, na daya daga cikin manyan ‘yan jaridar a Arewacin Nijeriya da yake da matukar sha’awar harkokin wasanni. Ya yi aiki da kamfanin jarida na New Nigeria Kaduna, amma tasirinsa da kwarewarsa sun yi matukar nisa.
Dansa, Sam; ya shiga aikin jarida bayan ya karanta fannin harhada magunguna (Pharmacy) a Jami’ar Obafemi Awolowo Ife, inda kuma ya yi aiki na dan wani lokaci a Kamfanin Pfizer. Canjin sana’a, na iya zama hadari; amma a nan ina tsammanin, wannan sauyi ya kasance mafi dacewa da kuma alhairi a cikin. Ya fara kasancewa ne tare da Kamfanin Jarida na Daily Trust a matsayin marubuci na-musamman (Columnists).
Tsakanin Shahara da Zama Sananne
Bayan ya kwashe shekaru a matsayin marubuci na-musamman, ya tattara rubutun nasa ya mayar da shi littafi mai suna ‘Nigeria’: wanda tuni ya shahara tun kafin ya kai ga kafa gidan jarida. Ya kunshi ayyuka da dama, koda-yake; kafin jaridar, ya fara wata jarida mai suna LEADERSHIP Confidential, wadda ta hada abubuwa daman a rayuwa, siyasa da kwazo a tsakanin manyan Abuja, ofisoshin jakadanci da kuma sauran ‘yan siyasa.
Ginshikan Jaridar Confidential
Farfesa Mahmood Yakubu, Malam Abba Kyari, Adamu Adamu, Mamman Daura, Abba Mahmood da kuma Adamu Suleiman, su ne suka fi sanin sirrin wallen gwamnati a wancan lokaci, wadanda kuma suka yi matukar bayar da gudunmawa. Amma Jaridar Confidential, ba ta ishi Sam ba; da yake mutum ne shi mai ra’ayoyin da tarin basira, don haka yana so ya ga ya yi abubuwa da dama.
Ya tattara kudaden day a samu ne bayan kaddamar da rubututtukan da ya yi ya mayar da shi littafi, kimanin Naira mliyan 20 a wancan lokaci tare da wata karamar tawaga da suka hada da Nnamdi Samuel, Abraham Nda-Isaiah, Uche Ezechukwu, Demola Abimboye, Winifred Ogbebo, Douglas Ejembi, Audee Giwa, Kingsley Chukwu, wadanda su ne ma’aikatansa na farko; ya fara fitar da samfur a karshen watan Satumbar 2004, kafin ya fara fitar kwafi a 4 ga Oktoba; inda ya sadaukar da ita ga Allah SWT da kuma kasa.
Sadaukarwa ga Allah da tasirin jaridar
Ba ni da tabbacin cewa ana karanta jarida a lahira, amma dai ko shakka babu; ‘yan Nijeriya sun karbi wannan jarida hannu biyu-biyu. Wasu fitattun jaridu, sun yi tasiri sosai a kan al’amuran kasashensu ta fuskoki masu kyau da kuma akasin haka. Lokacin da Rudolph Hearst ya fara jaridar New York, ya bayyana manufarsa a sarari: yadda aka fitar da Joseph Pulitzer na New York daga gari.
Wannan fafutukar, ta tunzura daya daga cikin mafi girman zamani a cikin aikin jarida na Amurka, gami da yadda Hearst ya yi amfani da jaridunsa, don haifar da mummunan rikici da Kasar Spain.
Duk da haka, ‘yan jaridu na Amurka su ma na da nasu jaruman, guda daga cikinsu ita ce, Katherine Graham; ‘yar wanda ya kafa ‘The Washington Post’.
Bindigar da aka dana harsashi
Ba ina cewa LEADERSHI ta fi kowace jarida ba, a’a, ina nufin jaridu na iya shafar yanayin al’amuran kasashensu ta bangarori daban-daban. Lord Beaberbrook da kakkausar murya ya bayyana cewa, “(Jarida na da matukar tasiri), domin kuwa tamkar wata takobi ce mai harshen wuta; wadda ka iya yanke duk wani makami da dan siyasa ke rike da shi, a nan ba wai ana nufin cewa; kowane babban kamfanin jarida zai iya tilasta wa gwamnati ta aiwatar da kudire-kudire ko hana ta yin abin da take son aiwatarwa ba, kawai saboda babban kamfanin jarida ne.
“Mafi yawancin ire-iren wadannan jaridu ba su da wata matsala, dalili kuwa ba su da wani lokaci da za su ce; bari su yi yajin aiki ko dakatar da ayyukan da sanya a gaba. Su kansu, bindigogi da harsashinsu a koda-yaushe yake a dane, suna kuma koya wa wadanda suke aiki tare da su yadda za su zuba wa bindigunsu harsashi da abin da za su rika harba suna mutuwa.”
Mafi karancin shekaru kuma wanda ya dade a kan karagar mulki, tsohon Firayim Ministan Burtaniya; Tony Blair, ya san haka. A tsawon shekarunsa na lamba 10, duk lokacin da dan jaridar nan Rupert Murdoch ya kira shi sau daya; sai ya amsa sau biyu.
Amma dai, ita LEADERSHIP ba kamar jaridar Sun ko Times Of London ba ce. Haka kuma ba Olusegun Obasanjo ko Blair ba. Har ila yau, Shugaban Kasar Nijeriya Obasanjo, ba zai manta da LEADERSHIP a kusa ba. A littafin tarihin Chidi Odinkalu da Aisha Osori, da muka karanta game da jajircewar shugaban kasar na yin takara karo na uku ba bisa ka’ida ba.
Alamun haske a koyaushe
Ko a kuruciyarta, LEADERSHIP kila ita ce jaridar da ta fi kawo wa Obasanjo cikas ga burinsa. Ta ci gaba da kasancewa tamkar wata annoba ga wasu karkatattun shugabanni a Nijeriya tare kuma da zama wata ginshiki ta hadin kan ‘yan kasa.
Misali, Imam Abubakar Abdullahi ya samu shahara ne bayan da kwamitin bayar da lambar yabo; suka amince da malamin sakamakon bai wa Kiristoci mafaka da ya yi a masallacinsa, daidai lokacin da rikicin addini ya barke a shekarar 2018 a Jos.
Bugu da kari, a bana ma; Auwalu Salisu mai tuka Keke mai kafa uku(Keke Napep) a Kano, jaridar ta karrama shi bisa mayar da Naira miliyan 15 da ya tsinta ga mai kudin, inda ya samu gagarumin yabo tare da kyautar Naira miliyan 250 daga Gwamnatin Jihar Neja, wanda Gwamna Mohammed Umar Bago ya yi alkawari ya kuma cika a karkashin kulawar gidauniyar Sam Nda-Isaiah.
Babu shakka, wannan jarida ta ci gaba da fafutuka wajen neman ‘yancin ‘yan jarida, ba tare da yin la’akari da abin da mayu ke yi; don ganin sun lalata ‘yan jaridar ba. Hukumar ta bi sahun wadanda ba a san ko su wane ne ba, wadanda suka kashe dan jaridar Nijeriya James Bagauda Kaltho a shekarar 1996, alal misali; ya kais hi wani dakin bincike na nakiyoyi daga Otal din Durbar da ke Kaduna, inda aka kai masa harin bam ta hanyar wani Russell Hanks; wanda ake kyautata zaton wakilin Amurka ne a Nijeriya, wanda ya koma ofishin jakadancin Amurka. Har izuwa yanzu dai, ba a warware batun wannan kisa ba.
Makwabci zuwa makwabci
Akwai kuma wani lokaci da ake yin maimaici. A kwanakin baya, bayan zaben 2015; tsohon Ministan Harkokin Neja Delta, Godsday Orubebe, ya yi wa Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa, Farfesa Attahiru Jega barazana; a daidai lokacin da ake bayyana sakamakon karshe, inda wani bangare na PDP da ke yi wa lakabi da Makwabci zuwa Makwabci, ya bai wa kamfanonin jaridu makudan kudade, domin su buga cewa Shugaba Goodluck Jonathan ne ya lashe zabe.
Haka nan cikin murna da jin dadi, wani ma’aikacin LEADERSHIP ya tattara wadannan kudade wuri guda ya kira Shugaban Kamfanin tare da shaida masa abin da ke faruwa. Sam, wanda fushinsa ko da a mafi kyawun lokuta, yana kasancewa ne tamkar wata mahaukaciyar guguwa. Nan da nan, cikin fushi; ya bayar da umarnin mayar da wannan kudi, ba a jima da mayar da kudaden ba; aka bayyana Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben, kuma Jonathan ya amince da shan wannan kaye.
Bangaren barkwanci na Ghana-Must-Go!
A cikin wadannan shekaru 20 masu ban sha’awa, masu karanta LEADERSHIP sun samu abokiyar tafiya wato, ‘Babba Da Jaka’ (Ghana-Must-Go), ma’ana; zane mai ban dariya a shafi na baya. A duk tsawon lokacin da na kwashe a nan, sau daya tak zan iya tunawa da aka soki wannan ‘Babba Da Jaka’ bisa rashin fahimta; a 11 ga watan Disambar 2020, lokacin da Sam ya kwanta dama. Zanen an yi shi ne ba kamar yadda aka saba yi ba, inda yak e nuni da cewa, rayuwar jarida da wadanda suka dogara da ita; na rataye a jikin wani zare.
Shekaru ashirin da suka gabata, sun kasance abin ban mamaki; tare da canjin da aka samu na kafofin watsa labarai, akwai kuma ci gaban da aka samu tare da rungumar fannin na’ura mai kwakwalwa, hauhawar farashin kayayyaki da kuma canza alkalumman al’umma; wadanda ke tilasta wa masana’antu sauya fasalin masana’antun nasu.
Duk da haka, a nan za mu iya cewa; tafiyar da ta fara a cikin dakin kwana sama da shekaru ashirin da suka wuce, ta samu ci gaba da taimakon Allah da kuma na mutane!
Allah ya kara jan zamaninta!
Ishiekwene, shi ne Babban Edita kuma Babban Mataimakin Shugabar Kamfanin LEADERSHIP, kana kuma marubucin sabon littafin koyar da rubutu a kafafen yada labarai da yadda za a samu kudi da shi (Writing For Media And Monetising It”