Dan wasan gaban Barcelona, Robert Lewandowski ya lashe kyautar dan wasan da ya fi zura yawan kwallo a raga a Nahiyar Turai.
Lewandowski ya zura kwallo 35 a kakar wasanni ta bara lokacin da yake kungiyar Bayern Munich.
- Qatar 2022: Babban Bankin Argentina Na Kokarin Sanya Hoton Messi A Takardun Kudin Kasar
- Yarjejeniyar Kare Mabambanta Hallitu a Duniya Ta Kunming Da Montreal Ta Fidda Wata Hanya Mai Dacewa a Fannin Kare Hallitu
Dan wasan mai shekaru 34, wannan karo na biyu da yake lashe kyautar.
Dan wasan dan asalin Kasae Poland, yanzu haka ya zura kwallaye 13 daga wasa 14 da ya buga a gasar Laliga ta Kasar Spain.
Da yake magana a wajen bikin karbar kyautar, Lewandowski ya bayyana farin cikinsa.
“Ina matukar farin ciki, na ji dadi sosai wannan kyauta na da muhimmanci a wajena.
“Na san ina da tarin aiki a gaba na amma hakan ba zai hana na nuna farin cikina ba,” in ji shi.