A wani yunkurin gaggawa na yaki da dabi’ar wulakanta kudi, hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), ta kama wata mata a Jihar Gombe, mai suna Janty Emmanuel saboda watsa takardun Naira a bainar jama’a a yayin wani biki.
A cewar kakakin EFCC, Dele Oyewale, an ga Janty Emmanuel tana watsa kudin a wurin taro na G-Connect da ke shiyyar Tumfure a jihar, a ranar Litinin 20 ga watan Mayu.
- Nijeriya Da Jamhuriyar Benin Za Su Sassauta Tsanantawa A Kan Iyakokinsu Ga ‘Yan Kasuwa
- Majalisa Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Dawo Da Wutar Lantarki A Arewa Maso Gabas
Nan da nan al’amarin wanda aka nada a faifan bidiyo ya karade shafukan sada zumunta abin da ya ja hankalin EFCC.
Ta hanyar yin amfani da bayyanan sirri, ba tare da bata lokaci ba EFCC ta cafke Janty Emmanuel domin amsa tambayoyi.
A yayin amsa tambayoyin, ta amsa aikata laifin.
Hukumar ta sha alwashin ci gaba da yakin da ta ke yi da wulakanta kudi, laifin da dokar Babban Bankin Nijeriya (CBN), ta tanadi hukunci akanta.
EFCC ta gargadin cewar ba za ta lamunci wannan dabi’ar ba kasancewar tana kaskantar da kimar takardar kudin Naira.
Janty Emmanuel za ta fuskanci tuhuma a kotu da zarar an kammala bincike akan lamarin, kuma idan an same ta da laifi, za ta fuskanci hukuncin tara ko dauri ko a hada mata duka biyun.
Al’amarin na zuwa ne biyo bayan shari’ar dan daudun nan, Idris Okuneye da aka fi sani da “Bobrisky”, da aka aikd gidan gyaran hali tsawon watanni shida bayan samun sa da laifin liki da takardun Naira.