Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya gana da babbar daraktar kungiyar cinikayya ta duniya WTO, uwargida Ngozi Okonjo-Iweala, wadda ke halartar taro na 7 na rukunin “1+6”, taron dake gudana a birnin Huangshan na lardin Anhui dake gabashin kasar Sin.
Yayin zantawar tasu a yau Alhamis, Li Keqiang ya ce, Sin na goyon bayan tsarin cinikayya na cudanyar sassa daban daban karkashin laimar WTO, tana kuma cika dukkanin alkawuran da ta dauka bisa sahihanci, tun bayan shigar ta kungiyar ta WTO sama da shekaru 20 da suka gabata, matakin da baya ga bunkasa Sin din da ya yi, a hannu guda, matakin na Sin ya taimakawa ci gaban sauran kasashen duniya.
Kaza lika, Li ya ce, a matsayin ta na kasa mai tasowa mafi girma a duniya, Sin za ta nacewa ka’idojin samar da daidaito, da bin ka’idojin WTO, za ta kuma tabbatar da sauke nauyin ta gwargwadon yanayin ci gaban tattalin arziki da ikon ta.
A nata tsokaci, uwargida Ngozi Okonjo-Iweala, ta jinjinawa gudummawar kasar Sin, da rawar da ta taka wajen ingiza tsarin cinikayyar sassa daban daban.
Ta ce warewar wasu sassa ba zai haifar da alfanu ga ci gaban tattalin arzikin duniya, da tsarin cinikayyar kasa da kasa ba. Jami’ar ta kara da cewa, WTO a shirye take ta karfafa hadin gwiwa da Sin, tare da hada kai da Sin din wajen daga matsayin tsarin cinikayyar kasa da kasa a bude, kuma bai cike da karsashi. (Saminu Alhassan)