Firaministan kasar Sin Li Qiang ya shaidawa shugaban kasar Amurka Joe Biden a gun taron kolin kungiyar G20 cewa, ci gaban kasar Sin wata dama ce, maimakon kalubale ga kasar Amurka, don haka ya kamata kasashen biyu su karfafa mu’amala a tsakaninsu.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ce ta bayyana hakan, Litinin din nan, yayin da take amsa wata tambaya mai nasaba da hakan da aka yi mata a yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa.
Mao Ning ta bayyana cewa, a lokacin da Li ya halarci taron G20, ya yi wata gajerewar ganawa da Biden da shugabannin wasu kasashe da dama.
A cewar Mao, Biden ya ce, bangaren Amurka na fatan tattalin arzikin Sin zai ci gaba da bunkasa, kuma Amurka ba za ta hana bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin ba.
Kana kuma Mao Ning, ta yi karin haske kan sakamakon taron kolin kungiyar G20 da aka gudanar a New Delhi na kasar Indiya, inda ta ce sanarwar shugabannin da aka fitar a taron, ta nuna matsayin kasar Sin.
Mao ta ce, yayin da ya halarci taron kolin G20 na New Delhi, firaministan kasar Sin Li Qiang ya yi karin haske kan ra’ayoyi da shawarwarin kasar Sin game da hadin gwiwar G20, yana mai ba da shawarar cewa, dukkan bangarorin sun tsaya tsayin daka kan ainihin manufar hadin kai da hadin gwiwa, tare da sauke nauyin dake wuyansu game da zaman lafiya da bunkasuwa, da zama abokan hadin gwiwa wajen inganta farfadowar tattalin arzikin duniya, da sa kaimi ga bude kofa da hadin gwiwa a duniya baki daya, da samar da ci gaba mai dorewa a duniya.
Taron ya fitar da sanarwar shugabannin, wanda ya nuna matsayin kasar Sin, kuma ya sanar da cewa, kungiyar G20 za ta dauki matakai ta hanyar hadin gwiwa, da aikewa da wata alama mai kyau ta G20 wajen yin hadin gwiwa don tinkarar kalubalen da duniya ke fuskanta, da inganta farfadowar tattalin arzikin duniya da ma ci gaban duniya baki daya.(Ibrahim)